’Yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna ƙauyen Illelar Dawagari da ke Unguwar Kagara, Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato, inda suka kuma harbe mutum guda tare da sace dabbobi sama da 200.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Daily Trust cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren Asabar.
Mazaunin ya ce ɗaya daga cikin mutanen da aka harba, Saminu Arzika, ya fita wajen ƙauyen ne domin bayan gida, inda ya hangi inuwar ’yan bindigar.
Ya ce Arzika sai ya haska musu tocila domin tabbatar da abin da ya gani, hakan ne ta sanya suka bi shi, kuma suka harbe shi. Ƙarar harbin ta sanya mazauna ƙauyen suka tsere zuwa cikin daji domin tsira.
Mazaunin ya ce maharan sun ci gaba da gudanar da ayyukansu har zuwa misalin ƙarfe 11 na dare, inda suka riƙa shiga gidaje ɗaya bayan ɗaya tare da kwashe dabbobi da adadinsu ya haura 200.
Ya ƙara da cewa ’yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane tara, waɗanda suka haɗa da maza biyar da mata huɗu.














