Aƙalla sojoji shida sun rasa rayukansu a daren Asabar bayan wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hare-hare a ƙauyen Kasuwar Daji da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce sama da mutane 75 ne kuma aka yi garkuwa da su a harin da aka kai a daren.
Majiyoyi sun shaida wa jaridar Vanguard ta wayar tarho cewa maharan sun kai hari ƙauyen Kasuwar Daji da misalin ƙarfe 11:30 na dare, bayan sun mamaye sansanin sojoji da ke yankin.
Majiyoyin sun yi zargin cewa sojoji shida sun mutu a harin, yayin da sama da mutane 70 aka yi garkuwa da su tare da tafiya da su cikin daji.
Wani mazaunin ƙauyen da ya bayyana sunansa a matsayin Alhaji Aminu Kasuwar Daji ya ce maharan sun shiga ƙauyen da yawa, inda nan take suka fara harbe-harbe ba kakkautawa domin kwace sansanin sojojin da ke yankin.
Hakazalika, tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Namadi Kasuwar Daji, ya tabbatar da kai harin a ƙauyen nasu, tare da tabbatar da cewa an yi garkuwa da wasu mazauna yankin, sai dai bai bayyana adadinsu ba.














