Iran ta musanta cewa tana gudanar da wata tattaunawa da Amurka, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa za a fara sabbin tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu daga ranar Litinin domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi, wanda yanzu ya shiga wata na shida.
Martanin na Iran ya fito ne ta bakin Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar, bayan Trump ya ce ya dakatar da shirin kai sabbin hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran domin ba da damar ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya.
Amurka da Iran na cikin rikici tun daga ranar 28 ga Fabrairu, lokacin da Amurka tare da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-haren ba-zata kan Iran. Sai dai an sha samun lokutan kwanciyar hankali sakamakon tattaunawar diflomasiyya da aka yi lokaci zuwa lokaci.
A makon da ya gabata, Trump ya yi barazanar kai wa Iran “mummunan hari”, inda rahotanni suka ce yana nazarin sake kai hare-hare, ciki har da kan cibiyoyin makamashi na ƙasar.
Sai dai a ranar Asabar, shugaban Amurkan ya dakatar da shirin, yana mai cewa an samu “ginshiƙan yarjejeniya” da za su iya kaiwa ga cimma matsaya.
Duk da haka, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta musanta cewa ana gudanar da wata tattaunawa da Amurka a halin yanzu.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Esmaeil Baqaei, ya ce yayin taron manema labarai na mako-mako, “Ba ma gudanar da wata tattaunawa da Amurka a halin yanzu. Tattaunawar da muke yi ita ce da Oman domin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa ta cikin mashigin ruwan Hormuz.”














