Alkaluman daga dandalin intanet sun nuna cewa, zuwa yanzu, jimilar kudin tikitin da aka saya na kallon fina finan kasar Sin a 2026, ciki har da wadanda aka sayar kafin fitowar fina finan, ta zarce yuan biliyan 23.
Baya ga haka, tun bayan kaddamar da kakar fina-finai ta lokacin zafi a ranar 1 ga watan Yuni, an fitar da fina finai sama da 120, wadanda suka shafi bangarori daban-daban kamar na tarihi da barkwanci da na fadace fadace da na kagaggun labaran kimiyya da kagaggun hotuna da sauransu, wadanda suka biya bukatun masu kallo.
Zuwa yanzu haka, kudin sayar da tikitin kallon fina finai a lokacin zafi ya zarce yuan biliyan 7.2. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/