ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 20, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Tattaunawar Neman Aiki…

by Sulaiman
1 month ago

Attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, kwanan nan ya halarci wata tattaunawa ta podcast mai suna ‘In Good Company’.

Tattaunawar ta fi mayar da hankali kan jarin da Dangote ke zubawa, amma yanayin tambayoyin da amsoshin da ya bayar, sai suka yi kama da irin waɗanda mai neman aiki ke bayarwa.

Tabbas ba neman aiki yake yi ba. An kiyasta arzikin Dangote ya kai kusan dala biliyan 30, kuma a cikin tattaunawar ya bayyana shirinsa na zuba jarin fiye da dala biliyan 45 a nahiyar Afirka.

ADVERTISEMENT

Amma shirin ‘In Good Company’, babbar nasara ce ga Dangote saboda kasancewar shirin, ya fi mayar da hankali ne kan manyan ’yan kasuwa, shugabannin duniya da fitattun masu tunani.

Dangote ya burge mai gabatar da shirin, Nicolai Tangen, da kwarin gwiwarsa da kuma shirinsa na zuba makudan kudade a Afirka, ciki har da gina daya daga cikin manyan cibiyoyin masana’antu a nahiyar — matatar mai ta dala biliyan 20 mai karfin tace ganga 650,000 a rana.

LABARAI MASU NASABA

Shari’ar Malami Ba Za Ta Dakatar Da Burinsa Na Gwamna Ba, Inji Jam’iyyar ADC Ta Kebbi

Kwamandojin Kungiyar Ansaru Biyu Sun Amsa Laifin Garkuwa Da Mutane A Kotu

Dangote ya nuna kwarewarsa sosai yayin tattaunawar, inda ya yi magana kan ladabi a kasuwanci, muhimmancin hangen nesa da kuma fahimtar bukatun kasuwannin Afirka.

A cewarsa, daya daga cikin manyan bukatun nahiyar shi ne samar da siminti, wanda kasashen Afirka da dama ke fama da karancinsa. Ya ambaci Nijeriya, Zambia da Congo Brazzaville a matsayin kasashen da suke zaman jira har watanni uku kafin su samu siminti.

Da aka tambaye shi inda ya samo kudin gina matatar mai, Dangote ya bayyana bayanai fiye da yadda ya saba yi. Game da bambance-bambancen al’adun kamfanoni a Afirka da wahalar gudanar da kasuwanci, Dangote bai raina nahiyar ba.

Maimakon haka, ya fi mayar da hankali kan al’adun aiki a cikin kamfanoni daban-daban da kuma matakin horas da ma’aikata, wanda ya ce za su iya yin nasara a duk inda suka shiga a fadin duniya.

Dangote har ya ambaci makarantar horaswa da kamfaninsa ke gudanarwa domin zakakuran dalibai daga jami’o’in Nijeriya da sauran kasashen Afirka.

Nicolai Tangen, ba kawai mai gabatar da podcast ba ne; shi ne babban jami’in gudanarwa na ‘Norges Bank Investment Management’, wanda ke kula da Asusun Arzikin Kasa na Norway.

Asusun na Norway shi ne mafi girman asusun gwamnati na zuba jari a duniya, inda yake da kadarori da suka haura dala tiriliyan 2.

Yana da hannun jari a kamfanoni 7,200 a kasashe 70 na duniya.Tattaunawar podcast din da Dangote ya yi wani bangare ne na tattaunawa da hadin gwiwar asusun domin zuba jari a Dangote da kuma Afirka baki daya.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Kimi K3 Ya Bayyana Yunkurin Sin Na Raya Fasahar AI A Bayyane Ta Yadda Kowa Zai Amfana
  • Sulaiman
    Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin A Saliyo Ta Fara Horar Da Ma’aikatan Jinya Dabarun Likitancin Gargajiya Na Sin
  • Sulaiman
    Binciken Pew: Me Ya Sa Sin Ta Fi Amurka Samun Anincewar Jama’a?
  • Sulaiman
    Cikakken Jerin Yan Wasan Da Suka Lashe Kyautuka A Gasar Kofin Duniya

MASU ALAKA

Shari’ar Malami Ba Za Ta Dakatar Da Burinsa Na Gwamna Ba, Inji Jam’iyyar ADC Ta Kebbi
Labarai

Shari’ar Malami Ba Za Ta Dakatar Da Burinsa Na Gwamna Ba, Inji Jam’iyyar ADC Ta Kebbi

July 20, 2026
Kwamandojin Kungiyar Ansaru Biyu Sun Amsa Laifin Garkuwa Da Mutane A Kotu
Manyan Labarai

Kwamandojin Kungiyar Ansaru Biyu Sun Amsa Laifin Garkuwa Da Mutane A Kotu

July 20, 2026
ICPC Ta Yi Karar Likitan El-Rufai Kan Ƙirƙirar Jabun Rahoton Lafiya
Labarai

ICPC Ta Yi Karar Likitan El-Rufai Kan Ƙirƙirar Jabun Rahoton Lafiya

July 20, 2026
Next Post
A Ƙarshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Dama Ta Yin Takara

Sojoji Sun Kama Wani Ɗan Sudan Da Ake Zargi Da Haɗa Kai Da ’Yan Ta’adda A Borno

Sojoji Sun Kama Wani Ɗan Sudan Da Ake Zargi Da Haɗa Kai Da ’Yan Ta’adda A Borno

July 20, 2026
Matashi Ya Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata Yayin Murnar Lashe Kofin Duniya Da Spain Ta Yi

Matashi Ya Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata Yayin Murnar Lashe Kofin Duniya Da Spain Ta Yi

July 20, 2026
Mbappé Ya Zama Mafi Yawan Ƙwallaye A Tarihin Gasar Kofin Duniya

Mbappé Ya Zama Mafi Yawan Ƙwallaye A Tarihin Gasar Kofin Duniya

July 20, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.