ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Ƙarshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Dama Ta Yin Takara

by Sulaiman and Naziru Adam Ibrahim
3 months ago
Jamilu Gwamna

Bayan samun goyon bayan Gwamnan Jihar Gombe, an amince da Jamilu Isyaku Gwamna, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a watan da ya gabata.

Yanzu a babban zaɓen 2027 Gwamna zai fafata da Bala Tinka na jam’iyyar ADC, da kuma Isa Pantami na jam’iyyar PDP, wanda dukkansu -Tinka da Pantami, sun koma sabbin jam’iyyunsu ne bayan sun gaza samun tikitin takara a APC.

Yayin da yake sanar da Gwamna a matsayin ɗan takarar APC, Gwamna Inuwa Yahaya, ya bayyana shi a matsayin gogaggen ɗan siyasa kuma ƙwararren ma’aikacin gwamnati da ke da karɓuwa a tsakanin al’umma, wanda a cewarsa Gwamna yana da amana da kuma tasirin da zai tabbatar wa jam’iyyar nasara a zaɓe mai zuwa.

ADVERTISEMENT

Da yake nuna godiyarsa kan wannan amana, Jamilu Gwamna, ya yi alƙawarin ci gaba da ɗora wa kan nasarorin da gwamnatin Jihar Gombe ta samu tare da ɗaga martabar jihar zuwa wani sabon matsayi na ci gaba.

Samun tikitin jam’iyyar APC mai mulki wani muhimmin sauyi ne a tafiyar siyasar Gwamna, wanda tun a shekarar 2007 ya fara neman kujerar gwamnan jihar Gombe ƙarƙashin jam’iyyar ANPP.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

A lokacin yaƙin neman zaɓensa na 2007, Gwamna ya ziyarci shalkwatar Kamfanin LEADERSHIP Group, inda ya bayyana burinsa da hangen nesansa na ci gaban Jihar Gombe.

Shekaru kusan ashirin kenan yana jiran wannan dama inda samun tikitin jam’iyyar mai mulki, wanda bai taɓa samu a baya ba, ya kusantar da shi ga cikar burinsa na zama gwamna, abin da ma sunansa “Gwamna” ke nuni da shi.

A shekarar 2011, ya shaida yadda ɗan uwansa, Ibrahim Dankwambo, ya bar aikin gwamnati a matakin tarayya tare da samun tikitin PDP, wanda ya kai shi ga zama gwamnan jihar.

Bayan shekaru takwas, yanayin siyasa bai ba da damar wani ɗan uwa ya gaji wani a kujerar gwamna ba amma daga bisani, a shekarar 2022, bayan ya kasa samun tikitin PDP, Jamilu Gwamna ya fice daga jam’iyyar tare da mara wa wa’adin mulki na biyu na Gwamna Inuwa Yahaya baya.

A wancan lokaci ma, Gwamna ya soki PDP, yana mai cewa jam’iyyar ba ta shirya karɓar mulki ba inda aka rawaito shi yana cewa; “A gare ni wannan mataki shawara ce ta kaina, tun da ban shirya yin ritaya daga siyasa ba, dole na nemi wata hanya, kuma wannan hanyar ita ce komawa APC.”

Duk da haka, ya jaddada cewa goyon bayan da ya bai wa Inuwa Yahaya, ba don wata buƙata ta kansa ba ne, sai dai saboda ci gaban jihar da kuma imaninsa cewa gwamnan na gudanar da aiki mai kyau kuma zai iya yin fiye da haka.

Yanzu alamu na nuna cewa wannan amincewa da goyon bayan da ya bai wa Gwamna Inuwa Yahaya, sun fara haifar masa da ɗa mai ido, domin gwamnan ya nuna masa irin wannan karamci ta hanyar mara masa baya domin samun tikitin takarar gwamna.

Jamilu Gwamna
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy
Jamilu Gwamna
Naziru Adam Ibrahim
+ posts Bio
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Ya Kamata Farashin Siminti Ya Sauka — Umahi Ga Masana’antun Siminti
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Yari Ya Dace Da Rayuwar Mulki Da Kasuwanci
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Shugaba Tinubu Ya Isa Nairobi Domin Halartar Taron Tattalin Arzikin Nahiyar Afirka
  • Naziru Adam Ibrahim
    https://hausa.leadership.ng/author/naziru-adam-ibrahim/
    Gwamnatin Filato Ta Kwato Kadarorin Jihar Da Aka Wawashe

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Me Kashim Imam Ke Yi A Yanzu?

Me Kashim Imam Ke Yi A Yanzu?

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.