Gamayyar Ƙungiyoyin Kare ‘Yancin Dimokuraɗiyya (CDR) a Jihar Bauchi, sun nuna rashin amincewa da kuma yin tsokaci kan yadda Kotun Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano ta yanke hukuncin da ya haifar da shakku da zargin yunƙurin danne haƙƙin zaɓen da ɗimbin jama’a su ka yi, bisa kyakkyawan tsarin dimokuraɗiyya.
CDR ta hasala ne dangane da hukuncin da kotun a Kano ta yanke, cewa, jam’iyyar mai mulki a ƙasa, APC ce da ɗan takarar a zaɓen gwamna a Kano su ka yi nasara, ba Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP ba, wanda INEC ta tabbatar.
- Kotun Zaben Gwamnan Taraba: Cikin Matsi INEC Ta Ayyana Sakamako, A Sake Bitar Zaben – NNPP
- Mun Dauki Darasi A Zaben 2023 – Shugaban INEC
“Akwai matuƙar buƙatar mu tunatar wa majiɓinta wannan al’amari da dukkan masu ruwa da tsaki cewa, Kano ita ce cibiya kuma ginshiƙin tattalin arzikin Nijeriya. “Don haka ƙoƙarin bijirowa ko cimma hargitsi na siyasa yanzu a Kano, abu ne da ka iya dagula wa ko tarwatsa jihohin Arewa.”
“A matsayin mu na gamayyar ƙungiyoyin yaɗa dimokuraɗiyya da kishinta da kuma kare martabarta, mun ga ya kamata mu fito don a ji muryoyinmu don ganin cewa ba mu sa-ido an yi wa al’umma ƙwacen abin da su ka zaɓa ba, lamarin da ka iya haifar wa Kano da Arewa baki ɗaya mummunan sakamakon za a yi da-na-sanin afkuwar sa daga baya.
“Mu na ƙara nuni da cewa, mu fa ba mambobin NNPP ba ne, kuma ba ‘yan asalin Jihar Kano ba ne, amma dai akwai haƙƙi a kan mu da wajibcin fitowa mu yi gargaɗi ga dukkan masu hannu kan shirin wannan lamari”
A lokacin da ya ke jawabi yayin wani jerin-gwanon lumana ɗauke da kwalaye a ‘Tafawa Ɓalewa Tomb’, Daraktan Tsare-tsaren CDR mai suna Ibrahim Babayo, ya ce, “Kyakkyawan tsarin dimokraɗiyya shi ne ginshiƙin ɗorewar ƙasa. Kuma abu muhimmi shi ne a kare darajar kowace ƙuri’ar da jama’a suka kaɗa bisa adalci.”
Ya ce babban adalci ga kotun zaɓe shi ne ta yi ƙwaƙƙwaran binciken duk wani zargin aikata ba daidai ba a lokacin zaɓe.