ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Ɗege Shari’ar Ganduje Da Wasu Mutum 7 Zuwa 14 Ga Oktoba 2026

by Abubakar Sulaiman
3 months ago
Ganduje

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

Babbar Kotun Jihar Kano ta ɗage shari’ar tsohon Gwamnan Jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa Hafsat Umar, da kuma wasu mutum shida zuwa ranar 14 ga watan Oktoba, 2026. An gurfanar da Ganduje ne tare da sauran waɗanda ake tuhuma kan zargi guda 11 da suka haɗa da cin hanci, da haɗin baki, da almundahana, da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai biliyoyin naira a lokacin da yake gwamna.

Sauran waɗanda ake ƙara a cikin wannan shari’ar sun haɗa da Abubakar Bawuro, da Abdullahi Umar, da Jibrilla Muhammad, da wasu kamfanoni guda uku da suka haɗa da Lamash Properties Ltd, da Safari Textiles Ltd, da kuma Lasage General Enterprises Ltd. Lokacin da aka dawo zaman kotun domin sauraron hujjoji da buƙatun da ke gaban kotun, lauyan gwamnati ya nemi izinin janye wata buƙata ta da can domin maye gurbinta da sabuwa.

Lauyan mai gabatar da ƙara, Mista Victor Oni, ya sanar da kotu cewa jihar a shirye take ta ci gaba da shari’ar, inda ya shigar da sabuwar buƙata ta ranar 15 ga watan Mayu, 2026, a matsayin martani ga lauyan wanda ake ƙara na shida ya shigar na neman a dakatar da shari’ar. Lauyoyin sauran waɗanda ake ƙara sun bayyana cewa su ma a shirye suke su ci gaba da fuskantar shari’ar.

ADVERTISEMENT

Sakamakon haka, mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta soke tsohuwar buƙatar mai gabatar da ƙara, sannan ta ɗege zaman kotun zuwa ranar 14 ga watan Oktoba domin sauraron abin da lauyan wanda ake ƙara na shida ya shigar. Wannan shari’a tana ɗaya daga cikin manyan shari’un da ke ɗaukar hankalin al’ummar Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya saboda nauyin zargin da ake yi wa tsohon gwamnan.

Ganduje
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati
  • Abubakar Sulaiman
    Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai
  • Abubakar Sulaiman
    Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

MASU ALAKA

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola
Manyan Labarai

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa
Manyan Labarai

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

September 13, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta'adda Kayan Aiki A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

September 13, 2026
Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

September 13, 2026
Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

September 13, 2026
Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

September 13, 2026
Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

September 12, 2026
Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

September 12, 2026
jam'iyyu

An Buƙaci Ƴan Takara Su Sanya Tsare-tsaren Yaƙi Da Ɗumamar Yanayi A Jaddawalin Kamfen Ɗinsu

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.