ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zarewa Ta Ƙirƙiro Na’urar Gano Tsatsa Bayan Lashe Kyautar ‘Carbon Neutrality’ Ta Duniya

by Muhammad
7 months ago
Zarewa

Manama, Bahrain — Ɗalibar digirin-digirgir (PhD) ‘yar Nijeriya daga Kano, Maimuna Umar Zarewa, ta lashe babbar kyautar duniya ta Carbon Neutrality Cup, bayan ta ƙirƙiro wata na’ura mai amfani da ƙirƙirarriyar basira (AI) domin gano lalacewar ƙarfe (corrosion/tsatsa) da kare muhimman kayayyakin more rayuwa na man fetur da makamashi.Zarewa

An shirya gasar ne ta hannun Gulf Petrochemicals and Chemicals Association (GPCA) a otel ɗin Sheraton da ke Manama, inda mahalarta daga ƙasashen yankin Hadaddiyar Daular Larabawa da suka hada da Qatar da Kuwait da Bahrain da Oman da kuma Saudiyya suka gabatar da sabbin dabaru kan dorewar muhalli da bunƙasar masana’antu.Zarewa

  • Waiwaye Adon Tafiya : Tasirin Sin A Kan Afirka Ta Fannin Fasahar AI
  • Majalisar ECOWAS Ta Shirya Fara Amfani Da Fasahar AI Don Inganta Ayyukan Dokoki

Zarewa, wadda ke karatun digirinta na uku a Jami’ar King Fahd University of Petroleum and Minerals (KFUPM) da ke Saudiyya, ta ƙera wata na’ura mai sarrafa kanta wadda ta haɗa shirya samfur (sample preparation), gano sinadarai, tsarin mutum-mutumin inji (robotics) da kuma nazarin bayanai ta hanyar basirar wucin gadi (AI) a cikin tsari guda.

ADVERTISEMENT

Sabuwar na’urarta ta bambanta da tsofaffin hanyoyin gano tsatsa (corrosion) da kan buƙaci na’urori da dama da kuma aiki da hannu. Ita kuwa, ta yi amfani da sinadari mai haske (fluorescence sensor) da aka samar daga tarkacen man fetur, wanda ke ba da damar gano lalacewa tun da wuri, cikin sauri, tare da rage kuɗaɗen aiki da dogaro da ma’aikata.

Ta hanyar mayar da tarkacen man fetur zuwa sinadari mai amfani, wannan ƙirƙire-ƙirƙire ya dace da manufar tattalin arziki mai zagaye (circular economy), tare da tallafa wa kare muhalli da rage gurɓacewar yanayi.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Bincike ya kuma nuna cewa sinadarin na da ikon hana tsatsa. A sakamakon haka, Zarewa na haɓaka sabon samfurin na’urar da zai ƙunshi tankin sinadarin kariya, wanda zai riƙa fesawa kai tsaye idan an gano alamun lalacewa, lamarin da zai sauya ta daga na’urar gano matsala kawai zuwa na’urar gano matsala tare da magance ta kai tsaye.

Masana sun ce asarar da tsatsa ke janyo wa masana’antar mai da iskar gas a duniya na kai biliyoyin daloli a kowace shekara. Sabuwar fasahar Zarewa na da damar taka muhimmiyar rawa wajen rage waɗannan asarori da ƙarfafa tsaron kayayyakin makamashi.

Nasararta ta ƙara haskaka rawar da matasan Nijeriya ke takawa a fannin binciken kimiyya na duniya, tare da nuna yadda sabbin dabaru ke taimakawa wajen tinkarar ƙalubalen muhalli da makamashi.Zarewa Zarewa

Zarewa
Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Buru

Ramadan: Coci Ta Raba Kayan Abinci Ga Makarantun Tsangaya A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.