Jami’an tsaro a Jihar Katsina sun kama wani mai sana’ar POS kuma ɗan kasuwar kayan gyaran babura, Isiyaku Nasiru, bisa zargin taimakawa wani fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Muhammadu, wajen gudanar da hada-hadar kuɗaɗe da ake dangantawa da ƙungiyar. An kama shi tare da wasu mutane uku a wurare daban-daban a Matazu da wasu yankunan da ke makwabtaka da ita tsakanin Alhamis da Asabar.
Sauran waɗanda aka kama su ne Abubakar Sayaya, da Nura Baka Sati da Ubale Mai Cange. Shugaban Ƙaramar Hukumar Matazu, Shamsuddeen Muhammad Sayaya, ya tabbatar da kamen, yana mai cewa ana ci gaba da binciken waɗanda ake zargin domin gano irin alaƙarsu da hanyar sadarwar ’yan bindigar.
Masu bincike sun yi zargin cewa Nasiru na sarrafa kuɗaɗen da suka kai tsakanin Naira miliyan uku zuwa biyar a kullum ta hanyar POS, inda ake zargin ana amfani da kuɗaɗen wajen sayen makamai, da harsasai da babura da ake bai wa ’yan bindigar.
Haka kuma, an zargi Sayaya da karɓar harsasai daga Ubale Mai Cange bisa umarnin wani kwamandan ’yan bindiga da ake kira Lawal, wanda aka fi sani da Yaya.
Nura Baka Sati kuma ana zarginsa da sayar da shanu ga ’yan bindigar tare da samar musu da abinci da sauran kayan tallafi. Rahotanni sun ce ana ci gaba da bin diddigin hanyoyin kuɗaɗen domin gano wasu mutanen da ka iya kasancewa cikin wannan hanyar sadarwa. Sai dai hukumomi sun jaddada cewa zarge-zargen da ake yi wa waɗanda aka kama na buƙatar cikakken bincike kafin a tabbatar da laifinsu.
Matazu na daga cikin ƙananan hukumomin Katsina da hare-haren ’yan bindiga da satar mutane suka fi shafa. Hukumomin tsaro na ci gaba da bincike kan waɗanda aka kama domin gano cikakken aikin da ake zargin kowannensu ya yi da kuma ko akwai wasu mutane da ke da hannu a cikin harkyallar.














