Mamallaki kuma daraktar gudanarwa ta cibiyar Bilmor, Bilkisu Magoro, ta gina wata cibiyar ilimi da koyon sana’o’i ga yara da matasa masu buƙatu ta musamman, wanda yake inganta damar samun rayuwa mai kyau a gare su.
Aiki a ƙasashe huɗu na nahiyoyi daban- daban, Bilkisu tana gudanar da babban jeri na ayyukan tallafi. Ita ƙwararriya ce a harkokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa, mamba ce a ‘African Business Roundtable’, mai fafutuka don ƙarfafa mata, kuma tana da tasiri sosai a harkokin siyasa a matakai da dama.
Sha’awar Bilkisu na tallafawa ya taso ne game da yadda samari da manya masu buƙata ta musamman ke zama kamar saniyar ware a cikin al’umma a wuraren zamantakewa da samun ayyuka yi, ta sa ta fara ilmantarwa da koya wa mutane da iyalai da dama masu buƙata ta musamman.
An kafa cibiyar Bilmor kusan shekaru goma kuma tana da hanyoyin horo na musamman da aka tsara, musamman don buƙatun ilimi na yara masu matsalolin koyo, kaggararuda kuma masu ƙalubale na halayya.Baya ga tsarin karatun makarantu, cibiyar Bilmor tana tsara ƙwarewar koyo ta musamman, tana ba da darussa a rubuce, koyon sana’o’i na rayuwa, tarbiyya da kuma fasahar magana da fahimtar harshe.
Kafin kafa cibiyar fasaha ta Bilmor a shekarar 2016, Bilkisu ta kafa gidauniyar Ismor Magoro a shekarar 2009, wata gidauniyar tallafa wa mata da matasa, wanda ya dace da manufofin ci gaba na Majalisar ɗankin Duniya.













