ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnati Ta Amince Da Inganta Cibiyar Kula Da Saran Maciji A Gwambe

by Sani Anwar
2 months ago
Amince

Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC), ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta amince da inganta cibiyar kula da saran maciji da ke garin Kaltungo a Jihar Gwambe zuwa “Cibiyar binciken cizon maciji ta ƙasa Kaltungo, a jihar ta Gombe.”

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate ne ya bayyana hakan, bayan taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC), a ranar Litinin da ta gabata.

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan taron, Ministan ya ce; majalisar zartarwa ta tarayya, ta yi la’akari da wasu muhimman abubuwa guda huɗu da suka shafi lafiyar ƴan Nijeriya tare da amince da haka.

ADVERTISEMENT

Pate ya ce, na farko shi ne; inganta cibiyar kula da saran maciji da ke Kaltungo a Jihar Gwambe zuwa cibiyar bincike da kula da cizon maciji ta ƙasa tare da faɗaɗa aikin kula da lafiya, horar da bincike don amsa buƙatu da kuma ba da kulawa mai kyau ga waɗanda maciji ya farwa.

Ministan ya lura cewa, cizon maciji ya kasance wani babban ƙalubalen kiwon lafiyar jama’a, musamman a yankunan karkara, kuma yana da matuƙar wahala ga masu rauni, manoma, makiyaya, mafarauta, mata da yara, waɗanda rayuwarsu da ayyukansu na yau da kullun, za su iya kai wa ga haɗuwa da maciji.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya ce, amincewar ta zama dole, saboda saran macizai na haifar da mutuwa, tawaya da raunin tunani tare da munanan yanayi na zamantakewa.

A cewarsa, “Wannan sabuwar cibiya, za ta kasance wata muhimmiyar cibiya da za ta tunkari ƙalubalen, musamman a shiyyar Arewa-maso-gabas da Arewa-maso-yamma, da kuma shiyyar Arewa-ta-tsakiya ta Nijeriya, inda lamarin ya fi ƙamari.

“Sabuwar cibiyar, za ta samar da cikakkiyar kulawa ta musamman ga saran maciji da sauran batutuwan da suka shafi gudanar da bincike a kan cututtukan da suka shafi maciji, rigakafi, tantancewa da magani, tabbatar da samun ci gaba mai ɗorewa da samar da ingantaccen maganin dafin maciji da kuma samun cikakken sashin asibiti da na likitanci, domin inganta kula da majinyata da ayyukan ƙwararru da sauran makamantansu.

“Haka zalika kuma, za ta yi haɗin gwiwa da cibiyoyin ƙasa da ƙasa. Wannan babban mataki ne da ya kawo wata cibiya da za ta kasance irinta ta farko a faɗin ƙasar nan, amma kuma a yankinmu.”

Pate ya kuma ce, abu na biyu shi ne; amincewa da sayen motocin asibiti guda 10 da ke ba da gudummawar jini, domin ayyukan shiyya na hukumar kula da jini ta ƙasa, don sauƙaƙa saye, tara da rarraba jini a kowace shiyya.

Ya ce, Nijeriya na buƙatar gudummawar jini kimanin miliyan 1.8 a duk shekara, inda ya ƙara da cewa; a halin yanzu, ƙasar na samun kusan kashi 25 zuwa 30 ne kacal.

“Za a iya tura waɗannan motoci na ba da gudummawar jini, don tara masu ba da gudummawa, ta yadda za mu inganta tarin jini mai muhimmanci ga mata masu juna biyu, ga waɗanda suka ji rauni da waɗanda aka yi wa tiyata ko kuma ga waɗanda ake yi wa tiyata, amma kuma ga waɗanda ake jinyar cutar daji, waɗanda ke buƙatar ƙarin jini ko wasu abubuwa na jini.

Amince
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Kano Pillars Ta Naɗa Mataimakin Kocin Super Eagles, Daniel Ogunmodede A Matsayin Sabon Kocinta

Kano Pillars Ta Naɗa Mataimakin Kocin Super Eagles, Daniel Ogunmodede A Matsayin Sabon Kocinta

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.