ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
Amurka

Ɗan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya ce gwamnatin Amurka ƙarƙashin Shugaba Donald Trump za ta sa ido sosai kan zabɓen Nijeriya da za a yi a 2027.

Moore, wanda ya kasance ɗan jam’iyyar Republican da ke wakiltar West Ɓirginia, a yayin da yake amsa tambayoyi game da zaɓen Nijeriya, ya bayyana yadda za a gudanar da zaɓen a matsayin batun da Washington za ta sa ido sosai a kai.

Ya yi waɗannan maganganun a cikin wata hira da gidan talabijin na Noire TƁ, wanda aka ɗora a shafukan sada zumunta a ranar Lahadin da ta gabata.

ADVERTISEMENT

Lokacin da aka tambaye shi ko Amurka za ta iya yin ƙarin abubuwa don tallafawa a samu sahihan zaɓe a Nijeriya, Moore ya ce, “Abin da zan ce shi ne, ina mai tabbas muku da cewa za mu saka ido wajen ganini sakamakon zaɓen da yadda zaɓe ke gudana da kuma yadda ake aiwatar da shi. Kuma wannan abu ne ni da gwamnati za mu mai da hankali sosai a kai.”

Ɗan majalisar dokokin Amurkan ya kuma bayyana cewa Majalisar Wakilan Amurka na duba wani ƙudirin kasafin kuɗi da ke ɗauke da wasu abubuwa dangane da Nijeriya, musamman kan ƴancin addini da taimakon tsaro na Amurka.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

“Muna aiki kan ƙudirin Chris (Smith), wanda a fili ina ɗaya daga cikin masu goyon bayan ƙudirin. Amma zan ce, mafi muhimmanci, abin da mutane suke buƙatar su kula da shi shi ne, ƙudirin kasafin kuɗi da za mu gabatar a majalisa a yau,” in ji Moore.

A cewarsa, ƙudirin dokar da aka bayar yana ɗauke da wasu batutuwa masu ƙarfi da tsanani game da dangantakar Nijeriya da Amurka.

“Akwai yawan maganganun da na saka a wannan ƙudirin da suka shafi Nijeriya kan tsangwama ga Kiristoci da kuma taimakon tsaro ga gwamnatin Nijeriya, da matakan da dole za su ɗauka.

“Wannan ƙudirin dokar na iya zama doka. Mun shiriya tare da fatan amince da shi a yau. Kuma haka nan akwai wasu kalmomi masu ƙarfi da tsauri a cikin wannan ƙudirin da za su zama wajibi dangane da dangantakarmu da Nijeriya a gaba,” ya ƙara da cewa.

Moore ya ce zai ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Trump kan batutuwan da suka shafi Nijeriya kuma ya bayyana cewa an tsara zai gana da shugaban ƙasar Amurka.

“Ina ci gaba da aiki tare da gwamnati kan matakan da za mu ɗauka na gaba. Gaskiya zan gana da Shugaba Trump a daren yau. Za mu ci abincin dare tare da shi da wasu ƴan majalisa, don haka, za mu ci gaba da tattaunawa da shi game da waɗannan batutuwa, kuma yana da matukar muhimmanci a gare shi,” in ji shi.

Moore shi ne ya fara gabatar da ƙudirin dokar ƴancin addini a Nijeriya ta 2026, wacce ya gabatar tare da ɗan majalisar dokokin Amurka, Chris Smith a watan Fabrairu.

Sabon ƙudirin dokar da ake shirin gabatarwa na nufin tilasta wa ministan harkokin wajen Amurka ya miƙa rahotanni lokaci-lokaci ga majalisar dokoki kan ƙoƙarin da ake yi don magance tsangwama ta addini da manyan ta’addanci a Nijeriya.

Ƙudirin dokar Smith da Moore na ba da shawarar a tantance yadda Nijeriya ke cika wajibai na ƴancin addini na duniya, taimakon tsaro na Amurka, takunkumi, tallafin jin kai, da matakan da gwamnatin Nijeriya ta ɗauka don kare al’ummomin da ke cikin haɗari da kuma gurfanar da masu kai hari.

Rahotanni sun bayyana cewa kwamitin majalisar Amurka a watan Afrilu 2026 ya amince da tanade-tanade da ke cikin ƙudin ƙarƙashin ma’aikatar harkokin waje da ke sanya ƙa’idoji masu tsauri da sharuɗɗa kan taimakon kuɗi ga Nijeriya.

Ƙudirin dokar, wadda aka tura wa majalisar dokokin Amurka don yin nazari, ta tanadin cewa kaso 50 cikin ɗari na kuɗaɗen da aka ware wa Nijeriya a ƙarƙashin sharuɗɗan taimakon ƙasashen waje za a dakatar da su har sai an tabbatar cewa gwamnati na ɗaukar matakai masu tasiri don rage tashin hankali na addini.

Haka nan kuma ƙudirin ya buƙaci kuɗaɗe da zai taimaka wa binciken da shari’ar tashin hankali da ƙungiyoyin Fulani suka aikata.

Ya ce dole ne gwamnati ta taimaka wajen dawo da mutanen da aka tilasta musu barin gidajensu cikin aminci.

Amurka
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Sin Ta Kalubalanci A Tabbatar Da Tsagaita Bude Wuta A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Kalubalanci A Tabbatar Da Tsagaita Bude Wuta A Gabas Ta Tsakiya

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.