Ɓangaren Sarki Aminu Ado Bayero ya nuna rashin jin daɗinsa tare da yin suka kan matakin Sarki Muhammadu Sanusi II na hawan doki zuwa wani taro a Jihar Kano, duk da umarnin da hukumomin tsaro suka bayar na hana gudanar da irin wannan hawa domin kiyaye zaman lafiya.
A cikin wata sanarwa da ɓangaren Sarki Aminu ya fitar, sun zargi Sarki Sanusi da saɓa wa dokar da aka shimfiɗa, inda suka bayyana cewa yin hawan doki zuwa wurin taron ya saɓa wa matakan tsaro da nufin kare birnin Kano daga shiga tashin hankali ko arangama tsakanin magoya baya.
Rikicin masarautar Kano dai ya sanya hukumomin tsaro a jihar suka sanya dokar hana dukkan ɓangarorin gudanar da hawan doki ko jerin gwano na sarauta a bainar jama’a, sakamakon takaddamar da ke ci gaba da wanzuwa kan karagar sarautar birnin.
Ɓangaren na Bayero ya buƙaci hukumomin tsaro da gwamnati da su tsawatar tare da tabbatar da cewa an hukunta duk wanda ya taka doka ba tare da nuna son kai ba, yana mai jaddada cewa bin doka da oda shi ne ginshiƙin tabbatar da kwanciyar hankali a jihar.
Kawo yanzu dai rundunar ƴansandan Jihar Kano da sauran hukumomin tsaro ba su ce komai ba a hukumance kan wannan ƙorafe-ƙorafe, yayin da jama’a ke ci gaba da zuba ido kan yadda takaddamar ke sauya salo tsakanin manyan ɓangarorin biyu.














