Rundunar ’yansandan Jihar Yobe ta kama wani yaro ɗan shekara 13 bisa zargin cinna wa gidan mahaifinsa wuta a Rugan Badali, a ƙaramar hukumar Karasuwa.
Mutane huɗu, ciki har da kishiyoyin mahaifiyarsa biyu da ƙannensa maza biyu, sun mutu a dalilin gobarar.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan mahaifin yaron ya yi masa duka bisa zargin satar kaza.
Yaron ya shaida cewa ya ɗauki kajin ne domin ya sayar, amma mutane suka sanar da mahaifinsa.
Yaron ya ce washegari bayan mahaifinsa ya masa duka, sai ya sayi ashanar Naira 50 sannan ya cinna wa gidan wuta yayin da matan mahaifinsa biyu da kannensa biyu ke barci.
Ya ce bayan wutar ta kama gidan, ya yi ihu domin neman taimako, kuma mutane suka zo don ƙoƙarin ceto waɗanda ke cikin gidan.
Sai dai yaron bai bayyana cewa shi ne ya kunna wutar ba sai bayan kwanaki uku.
Daga bisani ’yansanda suka kama shi tare da kai shi Damaturu domin ci gaba da bincike.
Kakakin ’yansandan Jihar Yobe, ASP Yusuf Adamu-Ali, ya ce duk da cewa yaron ƙarami ne, rundunar ba za ta yi watsi da lamarin ba. Ya ce za a ɗauki matakin da ya dace domin lamarin ya zama darasi ga sauran yara.














