ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

by Sulaiman
30 minutes ago
Siyasa

Yayin da zaɓukan kakar shekarar 2027 ke ƙara dumrowa, masu ruwa da tsaki a jihar Kaduna, sun gargaɗi musamman matasa da ƴan siyasa a jihar kan yin amfani da matasan domin yin jagaliyanci a lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma bayan zaɓukan.

Ɗaya daga cikin masu ruwan da tsaki, ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam da ke jihar, ta bakin Murshid a ƙungiyar kuma mai riƙon ƙwarya, a hirasa da LEADERSHIP Hausa ya ce ” Wannan zaɓe ne 2027, wajibi ne, mu gayawa mutane gaskiya, musamman kan yadda wasu ƴan siyasar, ke bai wa matasa ƙwayoyi da su kamar Gariyo, domin yi masu jagalanciyanci a lokacin zaɓukan,” A cewarsa, addinin Musulnci ya haramta aikata dabbacin siyasa duba da cewa, aikata hakan, na janyo rashin zaman lafiya kashe waɗanda ba su ji ba su kuma gani ba, domin kawai ƴan siyasa, cimma burukansu na siyasa.Murshid ya kafa hujja da Aya ta 5:32 a cikin suratul Al-Ma’idah da ta ce, kashe rai ɗaya, tamkar kashe alumma ce, baki ɗaya.

Ya ce, kamata yayi duk matashin da ya kira matasan su yi masa jagalanci, su ce masu, su bai wa ƴaƴansu su yi masu, inda ya ƙara da cewa, JNI za ta kuma bi ƴan siyasar su sheda masu cewar, duk wanda ƙungiyar ta samu ya bai wa matasan ƙwaya, Jama’atu wallahi, ba za ta barshi ba, idan har ta gane, ƴan siyasar, suna bai wa matasan Barandami da ƙwaya domin yi masu dabar siyasa.A ɓangaren addinin Kirista kuwa, fitaccen Fasto a Kaduna Dakta Yohanna Buru ya shedawa LEADERSHIP Hausa ya ce,”Babban saƙonsa akan wannan batun, ina gargaɗin ƴan siyasa kam yan da su daina amfani da ƴaƴan talakawa a matsayin ƴan dabar siyasa ko ƴan banga,” In ji shi.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, litaffin Bible mai tsarki, ya yi tir da akita dabar siyasa, wacce ke haddasa tayar da hargitsi a tsakanin alumma da kuma kashe rayukan jama’a, musamman duba da faɗin Aya ta, Matthew 11:12.Buru ya kuma yanko Ayoyin Isaiah 3:14 da Ezekiel 22:7, da suka yi tir da ɗabi’ar duk wani mai neman madafun iko da yayi amfani da ƙarfi k tuwo, kan tusawa marasa ƙarfi, domin samun shugabanci.

Ya jaddada cewa, idan har dabar siyasa abu ne mai kyau, kamata ya yi ƴan siyasar, su fito da nasu ƴaƴan su ba su makamai su yi dabar.Ya yi kira ga matasa da su farka daga baccin jahilci da fatara, su gane cewa, makomar rayuwarsu ta fi gaban dan kudin da ƴan siyasa ke basu na lokaci kalilan.Ita kuwa cibiyar sansanci a tsakanin addinai da ke a jihar Kaduna, ɗaya daga cikin Daraktocinta Mista Samson Auta a zantawarsa da LEADERSHIP Hausa gargaɗin kira ta yi ga matasan da su kaucewa yaɗa kalaman ƙiyaya a lokacin zaɓukan da bayansa, domin kaucewa haddasa yamutsi a cikin alumma.

LABARAI MASU NASABA

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Shi kuwa Darskta Janar na ƙungiyar da ke samar da kyakyawar alaƙa da haɗa kan alumimin A rewacin Nijeriya da kuma wanzar da zaman lafiya wato ACI Dakta Idris Abdullahi, a hirar da LEADERSHIP Hausa ya ce, ƙungiyar tun a farkon wannan shekarar ta fara wayar da kan matasa da ke a shiyyar Arewa maso Yamma, musamman ta hanyar gudanar da gangamin wayar da kansu, na ilolin kaucewa gujewa ƴan sisyar da za su ba su, kuɗi ƴan ƙalina domin yin dabar siyasa.

Kazalika, a ɓangaren masatsa ɗaya daga cikin ƴan majalisar Hakin Tudun Wada Kaduna wato garkuwan matasan yankin Alh. Nura Haruna ya ce, “Mu a gundumar yankin tuni, muka yi nisa wajen faɗakar da matasan da ke a yankin, wanda ya ce, yana da yaƙinin, ba za a tsinci matasan, a cikin wannan hali ba“ in shi.

Ya yi nuni da cewa, yawanci rashin aikin yi ne, ke sanya irin waɗanan ƴan siyasar ke yin amfani da wasu matasan domin jagaliyar siyasa.Shi ma wani shugaban matasan yankin Kawo a Kaduna Alh Murtala Umar Kawo ya ce, suma a yankin tuni, sun duƙufa wajen yin gangamin wayar da kan matasan yankin kan su gujewa bari a yi amfani da su, yin bangar siyasa.Ya ce, duk mutumin da ke tara ƴan daba, ana cin mutuncin mutane, musamman a lokacin zaɓe da ke hadda ɗaukar rayukan mutane ba ma tare da shi, a siyasa.

“Ina son matasan su gane cewa, irin waɗannan ƴan siyasar sun keɓe ƴaƴansu sun kuma kai su, makarantu masu tsada suna kula da rayuwarsu, amma su matasan ƴaƴan talakawa, suna nan suna yawo, abincin da ma za su ci, ya gagare su”. A cewarsa.

Ya ce, idan da matasa za su gane su rungumi sana’a da yafi masu, amma kar su bari, wasu ƴan siyasar su rinƙa basu ƙwaya da Tabar Wiwi da sauran kayan maye, kuma lokacin da za a fita yaƙin neman zaɓen su ɗauki makamai su shiga gaba domin yin dabar siyasa, bayan alhali su ƴan siyasar na cikin motocinsu suna shan isakar ACkuma a cikin motocin nasu suna cin dambun nama da madara, su kuma matasan, an bar cikinsu cike da hayaƙin kayan maye.

Shi ma Kwamandan NDLEA reshen Jihar Kaduna Muhammad Maijama, ya yi wannan gargaɗin, a hirarsa da LEADERSHIP Hausa inda ya ce,” Zamu sanya ƙafar Wando ɗaya, da duk wani mutum, ko matasan da ke shan kayan maye, a lokacin zaɓukan da kuma bayansu, domin yiwa ƴan siyasa a jahar dabar siyasa,” Inji shi.

A yanzu,“Mun ƙara ƙaimi na yin aiki ba dare ba rana, domin mu ci gaba da wayar da kan ɗaukacin alummar jihar, musamman matasan da ke yin tu’ammali da kayan maye cewar, duk wanda hukumar ta samu da hannu ya tayar da hankali a lokacin zaɓukan da kuma bayan zaɓukan, zai ɗanɗana kuɗarsa,” A cewar kwamandan.

Mai jama’a, ya ja hankalin musamman iyayen irin waɗannan matasan da ke yin tu’ammali da kayan maye, cewa, su, ja kunnen ƴaƴansu, domin duk wanda hukumar ta kama ya haddasa rikici a lokacin zaɓukan, zai fuskanci hukunci, kamar yadda dokar ƙasa, ta tanadar.

Siyasa
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa
  • Sulaiman
    Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa
  • Sulaiman
    Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

MASU ALAKA

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan
Labarai

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91
Manyan Labarai

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Gwamnatin Katsina
Labarai

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

September 12, 2026

LABARAI MASU NASABA

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

September 12, 2026
Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Gwamnatin Katsina

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

September 12, 2026
Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

September 12, 2026
Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.