ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: NDC Za Ta Duba Yiwuwar Dawo Da Tallafin Man Fetur Domin Sauƙaƙa Wa ’Yan Nijeriya

by Muhammad
1 week ago

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa domin rage farashin man fetur a Nijeriya, ciki har da dawo da tallafin man fetur idan ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Kano, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today, inda ya nuna damuwa kan yadda cire tallafin man fetur ya jefa ’yan Nijeriya cikin matsin tattalin arziki.

Ya ce har yanzu ’yan Nijeriya ba su farfaɗo daga girgizar tattalin arzikin da cire tallafin ya haifar ba, musamman saboda tsadar makamashi da hauhawar kuɗin sufuri da sauran kayayyakin masarufi.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, matsayar jam’iyyar NDC ita ce, dole ne a ɗauki matakan da za su rage wa al’umma nauyin tsadar rayuwa.

Kwankwaso ya ce: “Matsayar da muka cimma a yanzu ita ce farashin makamashi a wannan ƙasa ya yi yawa.”

LABARAI MASU NASABA

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta yi duk abin da ya dace domin rage farashin man fetur, har da sake duba batun dawo da tallafin.

Ya ce: “Matsayinmu shi ne za mu yi duk abin da ya dace domin tabbatar da cewa an rage farashin man fetur a ƙasar nan, ciki har da yin duk abin da za mu iya, har da batun tallafi.”

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa jam’iyyar ta tattauna kan matsalolin tattalin arzikin ƙasar, tare da yin la’akari da ƙwarewar manyan jagororinta, ciki har da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, da tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson.

Ya ce suna da ra’ayin cewa ya kamata a nemo hanyoyin da za su rage wa ’yan Nijeriya wahalhalun rayuwa.

Kwankwaso ya kuma nuna cewa ya kamata a magance cin hanci da rashawa a masana’antar man fetur domin taimakawa wajen rage farashin makamashi.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayun 2023, lokacin da ya karɓi ragamar mulkin Nijeriya.

Matakin ya haifar da ƙarin farashin man fetur da tsadar sufuri, tare da ƙara tsadar kayayyaki da ayyuka a sassa daban-daban na ƙasar.

Bayanin Kwankwaso na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke fara bayyana manufofinsu na tattalin arziki gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    2027: Matawalle Ya Bai Wa ’Yan Majalisar Zamfara Takwas Motocin Alfarma Kirar SUV
  • Muhammad
    UTME: Ɗalibai 108 Daga 39,000 ’Yan Ƙasa Da Shekaru 16 Ne Suka Cika Sharuddan Shiga Jami’a
  • Muhammad
    ’Yan Sanda Sun Kama ’Yan Ƙungiyoyin Asiri Takwas da Masu Damfarar ATM Uku A Kogi
  • Muhammad
    Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Ɗan Majalisa Na Watanni 3 Kan Fitar Bidiyon Jan Kunnen Zomo

MASU ALAKA

Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35
Manyan Labarai

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu
Manyan Labarai

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
Next Post
Hauhawar Farashin Kaya Ya Sauka Zuwa Kashi 14.63% A Watan Satumba — NBS

Hauhawar Farashin Kaya Ya Sauka Zuwa Kashi 14.63% A Watan Satumba — NBS

LABARAI MASU NASABA

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.