ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

by Sulaiman
4 weeks ago
Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa da kamfanin XEJet Limited domin fara zirga-zirgar jiragen fasinja kai tsaye tsakanin Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau da Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Yarjejeniyar Fahimtar Juna, wato MoU da aka sanya wa hannu ranar Litinin ta zama wani muhimmin mataki wajen inganta zirga-zirgar jama’a da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci, zuba jari, yawon buɗe ido da bunƙasar tattalin arzikin Jihar Zamfara.

Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni, ne ya jagoranci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ƙara da cewa, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammed Nakwada, ne ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) da kamfanin XEJet Limited kan bunƙasa hanyar zirga-zirgar jiragen sama, domin fara zirga-zirgar jiragen fasinja tsakanin Abuja da Gusau.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

“Ƙarƙashin yarjejeniyar, XEJet zai fara zirga-zirgar jirage sau biyu a kowane mako daga wata mai zuwa.

“Sabuwar hanyar zirga-zirgar jiragen sama za ta inganta damar zuwa Zamfara tare da buɗe ƙarin damammaki ga masu zuba jari, ’yan kasuwa da baƙi.”

Da yake jawabi a wajen bikin, Mataimakin Gwamna Mani Mummuni ya ce haɗin gwiwar ya yi daidai da manufar gwamnatin jihar ta inganta ababen more rayuwa na sufuri.

Ya ce, “An gina Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau ne tun daga tushe, kuma aka kammala shi cikin shekaru biyu.

“Babbar manufar gina filin jirgin shi ne sauƙaƙa tare da inganta zirga-zirgar mutane da kayayyaki, abin da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

“Gwamna Lawal yana ci gaba da neman masu zuba jari na ƙasa da ƙasa da hukumomin bayar da tallafi, waɗanda dukkansu suke da niyyar zuba jari a Zamfara.

“Wannan matakin fara zirga-zirgar jiragen kasuwanci zai jawo hankalin masu zuba jari. Inganta damar isa jihar ita ce babbar manufarmu, domin hakan zai samar da yanayi mai kyau ga bunƙasar kasuwanci da zuba jari.”

Gusau
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS
  • Sulaiman
    Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)
  • Sulaiman
    Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori Biyar

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi
Tsaro

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Uku Da Aka Sace A Kebbi

October 25, 2026
Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike
Labarai

Ana Buƙatar Ɗaukar Matakai Masu Tsauri Domin Ci Gaban Nijeriya – Wike

October 25, 2026
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Tura Dakarunta Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Yankin Olle-Bunu Na Jihar Kogi
Tsaro

Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 15 Ta Harin Sama A Borno

October 25, 2026
Next Post
El-Rufai: Yana Girbar Abin Da Ya Shuka Ne – Shehu Sani

2027: Hana Tinubu Wa’adi Na Biyu Na Iya Jefa Nijeriya Cikin Rikicin Siyasa — Pakistan

Tinubu Ya Cancanci A Sake Zaɓensa A 2027 — Pakistan

October 25, 2026
Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Taraba Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 40

October 25, 2026
Kwamitin Zartarwa Na ADC Na Ƙasa Ya Yi Watsi Da Bangaran David Mark Da Bala Gombe, Ya Naɗa Shugabancin Riƙo

ADC Ta Yi Wa APC Ba’a Kan Zargin Hayar Taron Jama’a Da Rashin Cika Kujeru A Taron Kaduna

October 25, 2026
An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.