ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abokin Jibi Shi Ne Aboki

by Sulaiman
3 months ago
Aboki

Hausawa su kan ce “Abokin jibi shi ne aboki”, saboda aboki na gaske ba wanda zai rika zuga ka ba ne, maimakon haka, zai iya ba ka taimako a lokacin da ka gamu da matsala.A kwanakin nan, an samu barkewar annobar Ebola a kasar Congo Kinshasa, inda mutane 321 aka tabbatar da kamuwarsu da cutar, kuma daga cikinsu wasu 41 sun mutu. An ce, kwayoyin cutar da suka haddasa annobar wannan karo, kwayoyi ne nau’in BDBV, wadanda har yanzu babu allurar rigakafi ko magani da za su iya dakile su, kana mutuwar mutane masu kamuwa da cutar ya kan kai kaso 25% zuwa kaso 38%. Sai dai ko da yake cutar na da matukar hadari, amma kasar Sin ba tare da wani jinkiri ba ta samar da taimako ga Afirka. A jiya, wasu kwararru masu ilimin likitanci 5 da kasar Sin ta tura sun isa birnin Kinshasa, inda suka fara samar da taimako a fannin hana yaduwar cutar Ebola a kasar Congo Kinshasa.

Mun san halayyar dan Adam ce, yin kokarin nisanta daga wurin da ake fuskantar wata annoba. Amma wadannan kwararru Sinawa cikin sani sun shiga wannan wuri mai fama da annoba. Hakan ya nuna zumuntar da ake samu tsakanin mutanen kasar Sin da na kasashen Afirka, wadda ta ba su ikon yaki da annoba kafada da kafada. A cewar Mista Lin Jian, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, kasar Sin da kasashen Afirka abokai ne na gaske, wadanda suka taba raba fara daya. Kana a kokarin tinkarar annobar Ebola ta wannan karo, kasar Sin za ta samar da tallafi ga kwamitin kungiyar kasashen Afirka ta AU, da ba da taimako ga cibiyar kandagarkin cututtuka ta nahiyar Afirka, a kokarin karfafa gwiwar kasashen Afirka ta fuskar tinkarar annoba.

Hakika kasar Sin da kasashen Afirka tuni sun taba gudanar da hadin kai a kokarin dakile cutar Ebola. Tsakanin shekarar 2014 da ta 2015, an samu yaduwar cutar Ebola a kasashen Saliyo, da Laberiya, da Guinea, inda kasar Sin ta tura kwararru kimanin 1200 zuwa wuraren da aka samu barkewar cutar don samar da taimako. Kana wadannan kwararru Sinawa sun yi jinyar mutane fiye da 900, da gudanar da gwajin jini na mutane fiye da 9000, da horar da jami’an lafiya fiye da dubu 13. Ban da haka, kasar Sin ta kafa cibiyoyin kula da masu fama da cutar Ebola a kasashen Saliyo da Laberiya, da gina dakin gwajin kwayoyin cuta mai matakin tsaron halittu na 3 a Saliyo, da samar da taimako ga kasashe 7 da suke makwabtaka da kasashen da suka samu barkewar annoba, wajen kafa tsarin hana yaduwar cuta, ta yadda kasar Sin ta samar da gudunmowa a yakin da kasashen yammacin Afirka suka yi da cutar Ebola a wancan karo.

ADVERTISEMENT

Sai dai tushen cimma nasarar yakar annoba shi ne amincewa da juna da aka samu tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, bisa hadin gwiwar da suka yi cikin dogon lokaci. Tun daga lokacin da kasar Sin ta tura tawagar likitoci ta farko zuwa kasar Aljeriya a shekarar 1963, zuwa yanzu kasar ta riga ta tura likitocinta kimanin dubu 26 zuwa kasashe 48 dake nahiyar Afirka, inda suka yi wa mutane miliyan 230 jinya. Kana a cikin dimbin shekaru da suka wuce, kasar Sin ta kafa asibotoci, da dakunan gwajin kwayoyin cuta, da sauran kayayyakin kare lafiyar jama’a a kasashen Afirka, gami da horar da jami’ansu na lafiya fiye da dubu 150.

Dalilin da ya sa kasar Sin gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya cikin dogon lokaci, shi ne manufar kasar ta gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya. A ganin kasar ta Sin, makomar mutane na mabambantan kasashe a hade suke. Muddin dukkan kasashe sun samu ci gaba, kuma dukkan al’ummun duniya sun samu rayuwa mai inganci, sa’an nan za a iya tabbatar da ci gaban al’ummar dan Adam mai dorewa.Batun shigar kwararru masu ilimin likitanci na kasar Sin cikin wurare masu fama da annobar Ebola dake kasar Congon Kinshasa, ya nuna zumunta, da kauna masu zurfi dake tsakanin bangarorin Sin da Afirka, da imaninsu kan hadin gwiwar da suke yi, a kokarin neman samun ci gaba na bai daya. (Bello Wang)

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Aboki
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
  • Sulaiman
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • Sulaiman
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.