ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

by Sulaiman
3 months ago
Mata

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana shirinta na tallafa wa mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu sama da miliyan daya a faɗin jihar, a wani mataki da ta ce zai ƙarfafa rayuwar al’umma tare da bunƙasa tattalin arziki.

An bayyana hakan ne a yayin wani taron kwana uku da aka gudanar a Sakkwato kan yadda za a aiwatar da Manufofin Ƙarfafa Tattalin Arzikin Mata na Ƙasa, wato Women’s Economic Empowerment Policy, a Jihar Zamfara cikin shekaru biyar masu zuwa.

Da take jawabi a wajen taron, Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma ta Jihar Zamfara, Dakta Aisha M.Z. Anka, ta ce shirin ya nuna ƙudurin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa mata da sauran rukunin jama’a masu rauni sun samu damar inganta rayuwarsu.

ADVERTISEMENT

Dakta Anka, wadda Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma, Alhaji Garba Aliyu Gayari, ya wakilta, ta bayyana cewa bunƙasa ilimin mata, kare haƙƙoƙinsu da kuma tabbatar da shigarsu cikin harkokin kuɗi zai taimaka wajen ƙarfafa iyalai da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a al’umma.

Ta ce gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta nuna aniyarta ta bunƙasa rayuwar mata ta hanyar manufofi da shirye-shiryen da ke ƙarfafa shigarsu cikin ilimi, noma, kiwon lafiya da shugabanci na siyasa.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

A cewarta, ba za a iya samun ci gaban tattalin arziki mai ma’ana ba tare da bai wa mata da ’yan mata damar cin gajiyar shirye-shiryen ci gaba ba.“Muna buƙatar ƙarin haɗin gwiwa daga Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya (World Bank) da sauran abokan hulɗar ci gaba domin tallafa wa matan Zamfara ta fuskar zamantakewa, siyasa da tattalin arziki domin samun ci gaba mai ɗorewa,” in ji ta.

Ta kuma buƙaci mahalarta taron da suka haɗa da wakilan hukumomin gwamnati, cibiyoyin gwamnati, ƙungiyoyin fararen hula, sarakunan gargajiya da shugabannin addini da su bayar da gudunmawa mai amfani wajen daidaita manufofin da yanayin rayuwa, al’adu da dabi’un al’ummar Zamfara.Tun da farko, wata ƙwararriyar mai ba da shawara da Shirin Kare Muhalli na Mata (WEP) ya ɗauka aiki, Misis Damaris Uja, ta ce an shirya taron ne domin ƙarfafa mata da matasa wajen samun damar amfani da haƙƙoƙinsu ta hanyar shirye-shiryen ci gaban muhalli, zamantakewa, siyasa da tattalin arziki.

Ta bayyana gurɓacewar muhalli, cin zarafin mata da rashin samun damar shiga harkokin kuɗi a matsayin manyan matsalolin da ke addabar mata da ’yan mata a sassa da dama na ƙasar nan.

A nasa jawabin yayin zaman nazari da tantance manufofin, jagorar taron, Farfesa Magdalyne Dura, ta ce aiwatar da manufofin wata alhakin gama-gari ce da ke buƙatar haɗin kan dukkan masu ruwa da tsaki.

Ta ce nasarar wannan tsari za ta dogara ne kan yadda masu ruwa da tsaki suka fahimci yanayin tattalin arziki da zamantakewar jihar tare da bayar da gudunmawa wajen samar da manufofin da za su dace da muradun al’ummar Zamfara.

Farfesa Dura ta kuma yi kira ga mahalarta taron da su tabbatar an tsara manufofin cikin tsarin da ya dace da al’adun gargajiya da kuma koyarwar addinin Musulunci da ake bi a jihar.A ƙarshe, mahalarta taron sun gabatar da shawarwari daban-daban domin samar da cikakkiyar manufa ta ƙarfafa tattalin arzikin mata, wadda za ta magance buƙatun mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu a Jihar Zamfara.

Mata
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP
  • Sulaiman
    Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire
  • Sulaiman
    Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 12, 2026
Mata
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Mata
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

LABARAI MASU NASABA

NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026
Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

Sin Tana Son Cin Moriya Tare Da Sassan Duniya A Fannin Kirkire-kirkire

September 11, 2026
Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

Sin Da Indiya Na Shirye-shiryen Ganawar Xi Da Modi

September 11, 2026
Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.