Zuwa yau Talata, jimilar adadin shige da fice da aka yi ta kafofin shiga da fita na birnin Beijing ya zarce miliyan 15, adadin da ya karu da kaso 9 kan mizanin shekara-shekara, inda ya kai wannan matsayin kwanaki 20 kafin lokacin samun wannan adadi a shekarar 2025.
Adadin shigowa Beijing daga kasashen waje ya kai miliyan 4.88 a wannan lokaci, karuwar kaso 31.6 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.
Saboda karuwar bukatar tafiye-tafiye a lokacin zafi, yawan fasinjoji a kafofin shiga da fita na Beijing ya ci gaba da kai wa sabon matsayi a kullum a watan Agusta, wanda ke ci gaba da zarce tafiye-tafiye 70,000 a kowace rana. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/