A yau Talata ne aka kaddamar da dandalin tattunawa na jami’an Sin da Amurka, mai lakabin “China‑U.S. Track 1.5 Dialogue” a nan birnin Beijing. Dandalin ya samu halartar wakilai daga ma’aikatun gwamnatin tsakiyar Sin, da na kananan hukumomin kasar, da kwararru daga sassa daban daban, da wakilai daga bangaren Amurka, ciki har da na bangarorin dake nahiyar Asiya.
Ana sa ran yayin taron, za a gudanar da tattaunawa mai zurfi dangane da batutuwan da suka jibanci inganta amincin siyasa, da fadada hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da lalubo sassan hadin gwiwa a fannin fasahar AI da kimiyya da fasaha.
Tun a shekarar 2023 ne aka kaddamar da dandalin, wanda ke taka rawa tsakanin wasu dandaloli biyu, watau na diflomasiyya ko “Track‑One diplomacy”, da na musaya tsakanin sassa masu zaman kansu, ko “non‑governmental Track‑Two exchanges”.
Dandalin na samar da muhimmin zarafi na tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasar Sin da na Amurka, da muhimman sassan al’ummu, da ’yan kasuwa, da masana da kungiyoyin al’umma.
Ya kuma sha gabatar da tarin shawarwari na bunkasa musaya da hadin gwiwar siyasa, da tattalin arziki, da cinikayya, da kimiyya da fasaha, da musaya tsakanin al’ummu da fannonin al’adu. (Saminu Alhassan)














