Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC-PCC ta buƙaci Majalisar Dokokin Tarayya ta yi watsi da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karɓar sabon bashi daga ƙasar waje na dala biliyan 20 da fam biliyan ɗaya, matuƙar gwamnatin tarayya ba ta bayyana cikakkun bayanai kan yadda za a yi amfani da kuɗin ba.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya fitar, ADC-PCC ta ce sabon bashin zai ƙara wa ƴan Nijeriya matsin tattalin arziƙi, waɗanda tuni suke fama da tsadar rayuwa da haraji. Ta kuma yi tambaya kan dalilin neman ƙarin basussuka ba tare da cikakken bayani kan yadda aka kashe kuɗaɗen bashin baya da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin man fetur ba.
Ologbondiyan ya ce gwamnati na buƙatar bayyana ayyukan da za a gudanar da kuɗin, yana mai tambayar inda hanyoyi, da wutar lantarki, da asibitoci, da ayyukan yi da sauran muhimman ababen more rayuwa da ya kamata irin waɗannan basussuka su samar suke. Ya yi gargaɗin cewa karɓar bashi ba tare da bayyana yadda za a kashe shi da sakamakon da ake sa ran samu ba na iya ƙara jefa ƙasar cikin matsalar basussuka tare da takaita damar gwamnatocin da za su zo nan gaba.
ADC-PCC ta buƙaci Tinubu ya fitar da cikakken rahoton dukkan basussukan cikin gida da na ƙasashen waje da gwamnatinsa ta karɓa tun ranar 29 ga Mayu, 2023, tare da bayanin kuɗin da aka samu daga cire tallafin man fetur da yadda aka kashe su. Ta kuma nemi a bayyana dalilan sabon bashin, da kuɗin ruwan dake akwai, da lokacin biya, da kuɗaɗen gudanarwa, da sharuɗɗan yarjejeniya da duk wata jingina ko garanti da ke tattare da shi.
Jam’iyyar ta yi kira ga ƴan majalisa da su yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba su wajen sa ido kan harkokin kuɗin gwamnati, tare da ƙin amincewa da bashin har sai gwamnati ta tabbatar da cewa lallai ana buƙatarsa, da dorewarsa da amfanin da ƴan Nijeriya za su samu.














