Ambaliyar ruwa ta tilasta wa ɗaruruwan mutane barin gidajensu tare da lalata gidaje da gonaki a sama da yankuna 18 a Karamar Hukumar Doma ta Jihar Nasarawa.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Nawani Aboki ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce mutanen da abin ya shafa sun nemi mafaka a wasu wurare da ke kan tudu.
Ya ce Gwamna Abdullahi Sule ya umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar da ta tantance asarar da aka yi tare da gabatar da rahoto.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnati na shirin samar da kayan agaji da kuma ɗaukar matakan hana ɓarkewar cututtuka.
Ya kuma gargaɗi waɗanda ambaliyar ta raba da muhallansu da ka da su koma gidajensu a yanzu, saboda fargabar ƙarin aukuwar ambaliyar ruwa sakamakon yiwuwar sakin ruwa daga Dam ɗin Lagdo da ke ƙasar Kamaru.














