ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

by Sulaiman
3 months ago
Iran

Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar a ranar Litinin cewa za ta dakatar da takunkumin tattalin arziki da aka kakaba wa Iran na ɗan lokaci, domin bai wa ƙasar damar samarwa, sayarwa da kuma jigilar ɗanyen mai da sauran kayayyakin man fetur har zuwa ranar 21 ga Agusta, 2026.

A cewar sanarwar, duk wata mu’amala da a baya aka haramta wadda ta shafi samarwa, sayarwa ko jigilar ɗanyen man fetur daga Iran za ta kasance halastacciya har zuwa ƙarfe 12:01 na dare agogon Gabashin Amurka a ranar 21 ga Agusta, 2026.

Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne saboda alƙawarin da Iran ta bayar a tattaunawar da ake yi tsakanin ƙasashen biyu.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, Iran ta amince da tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwa ta Hormuz, tare da bai wa masu Binciken Makamashin Nukiliya (IAEA) damar shiga ƙasar domin gudanar da ayyukansu.

Matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin sassauta rikicin da ya daɗe tsakanin Amurka da Iran, musamman kan batutuwan nukiliya, tsaro da harkokin makamashi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Masana na ganin dakatar da takunkumin na ɗan lokaci na iya ƙara yawan man fetur a kasuwannin duniya, lamarin da zai iya taimakawa wajen rage tashin farashin mai da kuma sauƙaƙa matsin tattalin arziki a wasu ƙasashe.

Iran
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
  • Sulaiman
    Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

MASU ALAKA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Sin Ta Kara Sassa 10 Na Kasar Amurka Cikin Jerin Bangarorin Da Ta Haramta Fitar Da Hajoji Zuwa Gare Su

Sin Ta Kara Sassa 10 Na Kasar Amurka Cikin Jerin Bangarorin Da Ta Haramta Fitar Da Hajoji Zuwa Gare Su

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Iran

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Iran

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.