Kamfanin BUA Foods Plc ya sanar da samun ribar bayan biyan haraji ta Naira biliyan 292.27 a rabin farkon shekarar 2026 da ta ƙare a ranar 30 ga Yuni.
Sakamakon ribar kamfanin na watanni shida ya nuna ci gaba mai ƙarfi, inda ingantaccen gudanar da ayyuka, ƙwarewar sarrafa harkoki da kuma rage kashe kuɗaɗe suka ƙara haɓaka ribar kamfanin a manyan rukunin kayayyakinsa.
Kamfanin ya bayyana cewa ribar bayan haraji ta kai Naira biliyan 292.27, wanda ke nuna ƙarin kashi 12 cikin ɗari idan aka kwatanta da Naira biliyan 260.1 da aka samu a daidai wannan lokaci na shekarar 2025.
Haka kuma, ribar kafin haraji ta ƙaru da kashi 14 cikin ɗari zuwa Naira biliyan 314.9, yayin da ribar gudanar da ayyuka ta haura da kashi 13 cikin ɗari zuwa Naira biliyan 320.5, lamarin da kamfanin ya danganta da ƙarfinsa na gudanar da ayyuka cikin tsari da ci gaba da inganta inganci.
Sai dai kudaden shiga (Revenue) na kamfanin sun ragu zuwa Naira biliyan 765.12, idan aka kwatanta da Naira biliyan 912.51 da aka samu a rabin farkon shekarar 2025. Kamfanin ya ce hakan ya faru ne sakamakon daidaita farashin wasu manyan kayayyaki duk da matsin tattalin arziki da hauhawar farashi.














