ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

DSS Da ‘Yan Sa-kai Sun Kashe Fitaccen Jagoran ‘Yan Bindiga Da Mayaƙansa Sama Da 60 A Katsina

by Sulaiman
1 month ago
DSS

Wani gagarumin samame na jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) bisa ingantattun bayanan sirri ya yi wa ayyukan ‘yan bindiga mummunar illa a Arewa maso Yamma, inda jami’an DSS tare da haɗin gwiwar masu sa-kai na al’umma da ƙwararrun mafarauta a Jihar Katsina suka kashe sama da mutum 60 da ake zargin ‘yan bindiga ne, ciki har da fitaccen jagoran masu garkuwa da mutane, Idi Abasu Aiki, a wani kazamin artabu a Ƙaramar Hukumar Bakori.

A rahoton da jaridar Tribune ta wallafa, ta bayyana cewa, majiyoyin tsaro sun ce Idi Abasu Aiki, wanda aka daɗe ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin ‘yan bindiga mafi hatsari a Katsina da maƙwabciyarta Zamfara, yana cikin waɗanda aka kashe a samamen da aka shirya bisa sahihan bayanan sirri.

A cewar majiyoyin, sama da ‘yan bindiga 200 masu ɗauke da manyan makamai, ƙarƙashin jagorancin Idi Aiki tare da goyon bayan mayaƙan da ke da alaƙa da fitaccen jagoran ‘yan bindiga Ado Aleru na Zamfara, sun kai farmaki ƙauyen Guga domin ɗaukar fansa kan al’ummomin da suke zargin suna ba jami’an tsaro da masu sa-kai bayanan sirri.

ADVERTISEMENT

An ce manufar harin na ‘yan bindigar shi ne, kashe jami’an tsaron al’umma da mafarautan da suka yi wa ƙungiyoyin ‘yan bindiga mummunar illa a wani artabu da aka yi a baya a ƙauyen Dawan Laila da ke Bakori, inda aka kashe sama da ‘yan bindiga 40.

Sai dai ba tare da sanin ‘yan bindigar ba, jami’an tsaro sun riga sun samu bayanan sirri kan shirin harin, inda suka shirya dakarunsu domin yi musu kwanton ɓauna.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Wata majiyar tsaro ta ce, “‘Yan bindigar sun faɗa tarkon da aka shirya musu. DSS ta samu sahihan bayanai tun kafin harin, sannan ta haɗa kai da masu sa-kai da mafarauta. Sama da ‘yan bindiga 60, ciki har da Idi Abasu Aiki da aƙalla manyan kwamandojinsa 14, an kashe su a artabun.”

Sai dai duk da nasarar da aka samu, an rasa rayukan mutum huɗu daga cikin masu sa-kai da mafarautan da suka taimaka wa jami’an tsaro a yayin fafatawar.

Bayan kammala artabun, jami’an tsaro sun gudanar da aikin share fage a yankin, inda suka kwato makamai da sauran kayayyakin da ‘yan bindigar suka bari yayin da suke guduwa.

DSS
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Giramamawa Ba Ta Samuwa Ta Kuskuren Taswira

Giramamawa Ba Ta Samuwa Ta Kuskuren Taswira

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.