Alkalin Babbar Kotun Jihar Kebbi da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi kwanaki bakwai da suka gabata, Mai Alkalin Faruku Hassan Bunza, ya samu ‘yancinsa kuma ya dawo gida lafiya.
Wani dan uwa na kusa da Alkalin ne ya tabbatar da sakin nasa ga wakilinmu a sanyin safiyar Litilin, inda ya ce Alkali Faruku Hassan Bunza ya iso gida ‘yan sa’o’i da suka gabata.
“Muna cikin farin ciki da murna tare da gode wa Allah bisa ganin namu ya dawo gida lafiya daga hannun ‘yan bindiga. An sake shi ne yanzu bayan ya cika mako guda a hannunsu,” in ji dan uwan.
Iyalin sun kuma nuna godiya ga duk wanda ya tsaya tare da su a wannan mawuyacin lokaci. “Muna mika sakon godiya ta musamman ga Alkalai da Ma’aikatan Shari’a na Jihar Kebbi, hukumomin tsaro, da al’ummar Jihar Kebbi baki daya da suka nuna damuwa, suka yi addu’a, suka kuma turo sakonnin jaje.
Haka kuma ya Kara da cewa, “Damuwarku da goyon bayanku sun ba mu karfi, muna godiya da hadin kan ku,” Inji dan uwan shi.
Dan uwan, ya ce, “sauran cikakkun bayanai kan yadda aka sake shi za mu bayyana daga baya”.














