Wani masanin tattalin arziki, Farfesa Akan Ekpo, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin karɓar sabon bashi har sai ta bayyana ayyukan da za ta gudanar da kuɗaɗen da kuma nazarin da aka yi kan su.
Ekpo ya bayyana cewa karɓar bashi ba laifi ba ne idan za a yi amfani da shi wajen gudanar da muhimman ayyukan raya ƙasa masu amfani, amma ya yi gargaɗin cewa rashin gaskiya da kulawar majalisa na iya jefa al’umma cikin wahalar biyan basussuka ba tare da amfana da ayyukan da aka yi alkawari ba.
Masanin ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin The Morning Show na gidan talabijin na Arise, inda ya ce ya kamata duk wani aikin da za a karɓi bashi domin gudanarwa ya kasance an yi masa nazarin fa’ida da asarar da kuma yiwuwar aiwatar da shi.
Ya ce gwamnati na bukatar bayyana taƙamaiman ayyukan da za a yi, musamman a ɓangaren samar da wutar lantarki, hanyoyi, tsaro, lafiya da ilimi, domin ’yan Nijeriya su iya ganin sakamakon amfani da kuɗaɗen cikin shekaru biyu zuwa huɗu.
Ekpo ya kuma bukaci Majalisar Tarayya ta kara tsaurara bincike da sa ido kan buƙatun karɓar bashi, tare da tabbatar da cewa gwamnati ta gabatar da dukkan takardun da suka dace kafin amincewa da su.
Ya yi gargaɗin cewa yara da jikokin ’yan Nijeriya ne za su gaji nauyin biyan basussukan da ake karɓa a yanzu, don haka bai kamata a karɓi bashi ba tare da samar da ababen more rayuwa da za su amfana da su ba.
A cewarsa, Nijeriya na bukatar ƙarfafa ɓangaren masana’antu domin ƙara samar da kayayyakin da za a fitar da su kasashen waje, samun kuɗaɗen shiga da kuma cimma burinta na gina tattalin arzikin mai yawa.














