An ayyana Sanata Sahabi Ya’u Kaura a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa.
Da yake sanar da sakamakon zaɓen a Gusau ranar Litinin, shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na mazaɓar, Dakta Auwal Abdullahi Aliyu, ya ce ’yan takara uku ne suka fafata.
Ya bayyana cewa Sahabi Ya’u Kaura ya samu ƙuri’u 49,176, yayin da Alhaji Tijjani Yahaya ya samu 9,628, sannan Sani Abdullahi Shinkafi ya samu ƙuri’u 2,602.
Dakta Auwal ya ce bayan tantance dukkanin ƙa’idojin kundin tsarin mulki da kuma dokokin APC, an ayyana Sahabi Ya’u Kaura a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin bisa yawan ƙuri’un da ya samu.














