An bude bikin fina-finai na Changchun na kasar Sin karo na 21, a cibiyar fina-finai ta kasa da kasa a birnin Changchun na lardin Jilin, a daren jiya 23 ga watan Agusta, wanda babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG da gwamnatin lardin Jilin suka shirya tare.
Wannan bikin fina-finai ya mai da hankali matuka ga sabbin halaye da kuzarin matasa da kuma karfin fina-finai. A gun taron bude bikin, an yi raye-raye don girmama kamfanin samar da fina-finai na Changchun, wanda aka yi masa lakabi da “mahaifar fina-finan jamhuriyyar jama’ar Sin”.
Bugu da kari, an nuna wurare mafi muhimmanci a tarihin fina-finai a Changchun ta amfani da taswirar tauraron dan adam, kuma masu sa kai a sha’anin fina-finai sun yayata jigon biki, wato “Kaunar fina-finai da kaunar wannan birni”.
Kazalika, an hade hotuna da bidiyoyi na gargajiya da wadannan wuraren birni da rayuwar jama’a ta zaman tare, ta hanyar sada fim da abubuwa masu nasaba, don yada muhimman ruhohin JKS da burin fina-finai.
Bikin fina-finai na Changchun na kasar Sin karo na 21 zai dauki tsawon kwanaki 6 ana yi, kuma za a gudanar da tarurruka na musamman kamar na “dare mai kayatarwa kan nuna AIGC da bikin karramawa” da kuma ayyuka masu ban sha’awa ciki har da” tattarawa da nuna gajerun fina-finai na daliban jami’a” da sauransu. (Amina Xu)














