An kaddamar da fara aikin gina cibiyar warkar da masu fama da cutar daji bisa tallafin kasar Sin a Tunisia, jiya Lahadi a birnin Gabes da ke kudu maso gabashin kasar.
A yayin bikin kaddamar da fara aikin, Walid Naija, babban darektan kiwon lafiya a ma’aikatar harkokin lafiya ta Tunisia, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, Tunisia da kasar Sin na morar kyakkyawar alaka a tsakaninsu kuma suna ci gaba da amincewa da juna sosai.
Ya bayyana cewa, kaddamar da fara wannan aiki na nuna hadin gwiwa mai karfi da ke ci gaba da bunkasa a tsakanin kasashen biyu, inda ya kara da cewa, da zarar an kammala, cibiyar za ta bai wa mazauna yankin kudu maso gabashin kasar ta Tunisia damar samun ingantacciyar waraka tare da kulawa mafi gamsuwa.
Liang Gang, jami’in da ke kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Sin da ke Tunisia, ya ce fara wannan aiki wani kwakkwaran mataki ne na karfafa hadin gwiwa mai amfanarwa a tsakanin kasashen biyu, tare da nuna shaida baro-baro a fili game da kyakkyawar alaka mai zurfi da ke tsakanin al’ummomin kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













