Za a gudanar da baje kolin cinikayyar hidimomi ta kasa da kasa ta kasar Sin (CIFTIS), a birnin Beijing daga ranar 9 zuwa 13 ga watan Satumba. A cewar mashirya baje kolin, an bude kafar rejista ga ‘yan jarida daga yau 10 zuwa 26 ga watan nan na Agusta.
‘Yan jarida za su iya shiga shafin yanar gizo na CIFTIS watau (www.ciftis.org), su danna sashen yin rejista na “Exhibit & Participate- Media Registration” domin kammala aikin.
Daga bisani, za a sanar da lokaci da tsarin karbar shaidar rejistar ga manema labarai a bangaren yada labarai na shafin yanar gizo na CIFTIS. (Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT














