Hukumar kula da shige da fice ta kasar Sin ta bayar da rahoton cewa, an samu shigowar baki kasar Sin sau miliyan 22.91 a rabin farko na bana, adadin da ya karu da kaso 20.4 kan mizanin shekara-shekara, inda shigowar da aka yi ba tare da visa ba, ya dauki kaso 77.7 na jimilar.
Ko mene ne dalilin da ya sa ziyartar kasar Sin ke kara samun karbuwa a wajen al’ummun duniya?
A baya-bayan nan, kalmomi kamar na “China Travel” da “China Cool”, wadanda ke nufin ziyartar kasar Sin, na ta samun karbuwa a kafafen sada zumunta biyo bayan yadda baki da ke ziyartar kasar ke wallafa bayanai da hotunan bidiyo game da ziyararsu. A ganina, wannan ba ya rasa nasaba da wasu batutuwa kalilan da zan zayyano:
Na farko, manufar bude kofa ta kasar Sin ta shafi kusan kowanne bangare, har da yawon bude ido. Yayin da ake ganin shingayen hana baki ziyartar kasashe da yadda ake kara nuna kyamar baki a manyan kasashe da mayar da wasu saniyar ware, kasar Sin ta bude kofarta ga al’ummun kasashen waje, inda a kullum take maraba da baki su ziyarci kasar don su more damarmaki, su ga irin ci gabanta da fahimtar tsare-tsaren raya kai da ta zabar wa kanta. Haka kuma, ta saukaka hanyoyin shiga kasar inda zuwa yanzu, ta gabatar da damar shigowa kasar ba tare da visa ba ga kasashe 5o, kana ta rattaba hannu kan yarjeniyoyin soke visa tsakaninta da kasashe 29. Haka kuma, matafiya daga kasashe 55 za su iya shigowa kasar su yada zango na tsawon sa’o’i 240 ba tare da visa ba, ta kafofi 65 na shiga kasar. Watau dai, matakin bude kofar ba abu ne da ya tsaya a kan takarda, ana kuma samar da dimbin damarmaki da aiwatar da matakai ta yadda matafiya za su shigo cikin sauki.
Abu na biyu, daya daga cikin abubuwan da ke jan hankali shi ne ingantaccen tsarin sufurin kasar Sin da ya game biranen kasar. Ga sauki, ga sauri ga kuma inganci, lamarin da ke saukakawa matafiya zirga-zirga a kasar.
Abu na uku, idan aka kwatanta da sauran kasashe, kasar Sin ta fi sauki da arhar rayuwa. Ba matafiya kadai ba, ko baki mazauna da suka shafe shekaru a kasar Sin sun tabbatar da cewa, kusan farashin abubuwan da suke saye a yau da kullum, ba sa hauhawa kamar yadda ake ganin hauhawar farashin kayayyaki da na rayuwa a sauran sassan duniya.
Abu na 4 shi ne abun da na sha nanatawa watau tsaro. Kowa ya shaida cewa, kasar Sin kasa ce da al’ummarta ke matukar more kyakkaywan tsaro. A ko da yaushe, za ka iya yawo ba tare da fargabar wani mugun abu ba, haka kuma kayanka ba za su taba bata ba, sai dai a adana maka. Tabbas wannan yana nuna dabi’a ta gari ta Sinawa da kuma wadata da kwanciyar hankali da ke akwai a kasar.
Ba shakka duniya na kara shaida karfi da ci gaban da ta samu a fannonin raya kasa da suka shafi kyautata rayuwar al’umma da ba su kariya da wadata da karfin tattalin arziki. Sin ta kara nuna wa duniya cewa, rufe kofa da nuna kyama a yanayin da duniya ke ciki yanzu, ba za su haifar da da mai ido ba. Bugu da kari, ta nuna a aikace cewa, niyyarta ita ce samun al’ummar duniya mai jituwa da fahimta da makoma ta bai daya. (Fa’iza Mustapha)














