An ceto masu yi wa kasa hidima 10 (NYSC) da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su daga dajin Egume da ke Karamar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi, a wani samame na hadin gwiwa da ’yansanda, sojoji, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da sauran jami’an tsaro suka gudanar.
Rundunar ’Yansandan Jihar Kogi ta bayyana a cikin wata sanarwa da kakakinta, ASP Saliu Oyiza Afusat, ya fitar jiya cewa, an samu nasarar ceto wadanda aka yi garkuwa da su ne bayan gudanar da wani aikin tsaro na hadin gwiwa, biyo bayan samun bayanan sirri.
Rundunar ta ce aikin ceton har yanzu yana ci gaba, inda jami’an tsaro ke kara kaimi wajen gano tare da ceto sauran mutanen da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutanen suna tsare da su.
A cewar sanarwar, aikin na da nufin tarwatsa kungiyoyin masu aikata laifuka da ke gudanar da ayyukansu a yankin, tare da gurfanar da wadanda ke da hannu wajen sace mutanen a gaban kotu.
Kwamishinan ’Yansandan jihar ya yaba wa jami’an ’yansanda, sojoji, DSS da sauran jami’an tsaro da suka taimaka wajen gudanar da aikin, bisa jarumtarsu, kwarewarsu da jajircewarsu wajen ganin an ceto wadanda aka yi garkuwa da su.














