ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 19, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Dakatar Da Jami’an NSCDC 21 Kan Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

by Abubakar Sulaiman
6 hours ago

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da jami’an Hukumar Tsaro na Sibil Difens (NSCDC) 21, ciki har da Kwamandan hukumar na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, tare da kafa kwamiti mai mutum 10 domin binciken mutuwar mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda suka mutu a hannun hukumar a Minna.

Matakin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gudanar da cikakken bincike ba tare da katsalandan ba.

Daga cikin jami’an da aka dakatar akwai:

ADVERTISEMENT

SC Usman Isah Ndamaka

ASCI Hassan Mohammed

LABARAI MASU NASABA

Motoci Masu Amfani Da CNG Da Lantarki Sun Rage Kuɗin Sufuri Da Kashi 83 – Tinubu

Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Ƴan Kasuwa 3 A Filato

CCA Bala Mohammed

CSC Oluwadare Sunday

DCC Obafemi Elvis

CSC Annas Shitto Lamino,

DCC Philip Ajayi

Barr. Stephen Tsado

ASCI Alhassan Mohammed

IC Abdullahi Sale

IC Mohammed Sonfada

CAI Liman Abubakar

CAI Bala Usman

IC Mohammed Jiya

DSC Isah Suleiman

CAI Ahmed Wushishi

IC Sale Adamu

IC Haruna Mohammed

ASCI Aliyu Sallah da

CAI Isah Sanusi, baya ga Kwamanda Aniviye. Ana binciken rawar da jami’an suka taka wajen kamawa, da tsarewa da kuma kula da mutanen da suka mutu.

Kwamiti mai mutum 10 da aka kafa zai samu jagorancin Jonathan Kure, tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar DSS, yayin da Farfesa Isa Hayatu Ciroma, SAN, tsohon Darakta-Janar na Makarantar Koyar da Lauyoyi ta Nijeriya, zai kasance sakataren kwamitin.

Sauran mambobin sun haɗa da AIG Hosea Hassan Karma (mai ritaya), da Farfesa Olayinka Buhari, da wakilin Majalisar Masarautar Minna, da wakilin Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Liman Sulaiman na ƙungiyar masu haƙar ma’adinai ta ƙasa (Miners Association of Nigeria), da Deji Adeyanju, da Zainab Suleiman Okino da Dr George Agbakahi.

An ɗora wa kwamitin alhakin gano sunayen waɗanda suka mutu, da binciken yadda aka kama su da kuma yanayin da aka tsare su, da kuma gano musabbabin mutuwarsu. Haka kuma, kwamitin zai binciki ko akwai sakaci, ko laifi ko wani alhaki daga jami’an da abin ya shafa, tare da bayar da shawarwarin matakin da ya kamata a ɗauka da kuma yiwuwar diyya ga waɗanda abin ya shafa. An ba kwamitin makonni biyu ya kammala bincikensa ya gabatar da rahoto ga Ministan Harkokin Cikin Gida.

Mutuwar mutanen 37 ta faru ne bayan da NSCDC ta kama waɗanda ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto na Jihar Neja a ranakun 15 da 16 ga Satumba, 2026. NSCDC ta ce a farko mutanen sun mutu ne sakamakon zargin ɓarkewar wata cuta, amma bincike da gwaje-gwajen lafiya ne kawai za su tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Ƴan Kasuwa 3 A Filato
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 12, Sun Ceto Mutane 66 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    Ku Rage Farashin Mai, Ku Sakarwa Ƴan Nijeriya Mara – Atiku Ga Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

MASU ALAKA

Motoci Masu Amfani Da CNG Da Lantarki Sun Rage Kuɗin Sufuri Da Kashi 83 – Tinubu
Manyan Labarai

Motoci Masu Amfani Da CNG Da Lantarki Sun Rage Kuɗin Sufuri Da Kashi 83 – Tinubu

September 19, 2026
Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Ƴan Kasuwa 3 A Filato
Labarai

Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Ƴan Kasuwa 3 A Filato

September 19, 2026
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 12, Sun Ceto Mutane 66 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Labarai

Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 12, Sun Ceto Mutane 66 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

September 19, 2026
Next Post

Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Angola: Kasar Sin Tana Da Shugaba Mai Hangen Nesa

Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Angola: Kasar Sin Tana Da Shugaba Mai Hangen Nesa

September 19, 2026
2027: Magoyin Bayan Atiku Ya Fice Daga ADC, Ya Goyi Bayan Tinubu

2027: Magoyin Bayan Atiku Ya Fice Daga ADC, Ya Goyi Bayan Tinubu

September 19, 2026
Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Ƴan Kasuwa 3 A Filato

Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Ƴan Kasuwa 3 A Filato

September 19, 2026
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 12, Sun Ceto Mutane 66 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 12, Sun Ceto Mutane 66 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

September 19, 2026
An Dakatar Da Jami’an NSCDC 21 Kan Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

An Dakatar Da Jami’an NSCDC 21 Kan Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

September 19, 2026
Ku Rage Farashin Mai, Ku Sakarwa Ƴan Nijeriya Mara – Atiku Ga Tinubu

Ku Rage Farashin Mai, Ku Sakarwa Ƴan Nijeriya Mara – Atiku Ga Tinubu

September 19, 2026
Portugal Ta Gayyaci Ronaldo Gasar UEFA Nations League

Portugal Ta Gayyaci Ronaldo Gasar UEFA Nations League

September 19, 2026
Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

September 19, 2026
Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa

Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa

September 19, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.