Ƴan bindiga sun kai hari wata kasuwar kayan lambu a garin Mangu, Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren Juma’a, lokacin da ƴan kasuwa da masu sayayya ke shirin rufe kasuwar.
Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Mwaghavul (MDA), Bulus Dabit, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce maharan sun buɗe wuta kan wata mota da ke barin kasuwar. Ya ce harbin ya kashe mata biyu da wani matashi namiji, yayin da ba a kai ga gano sunayen waɗanda aka kashe ba.
Dabit ya ce wasu daga cikin mutanen da ke kusa da wurin sun samu munanan raunuka, ƙarar harbin ya sa mutane suka ruga a guje domin tsira, lamarin da ya janyo ƙarin raunuka. An ce ana tura wasu daga cikin waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) domin kula da su.
Wani mutum mai suna John Haruna, wanda shi ma ya tabbatar da harin, ya ce harbin kan mai uwa da wabi ya jefa kasuwar cikin ruɗani, inda mutane suka riƙa gudu ta ɓangarori daban-daban. Dabit ya yi kira ga hukumomin tsaro da su yi amfani da bayanan sirri da fasahar zamani wajen gano waɗanda suka kai harin tare da cafke su.
Harin ya zo ne sa’o’i kaɗan bayan MDA ta bayyana damuwa kan barazanar tsaro da ke ci gaba da fuskantar al’ummomin Mangu, inda ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa sama da ƴan ƙabilar Mwaghavul 750 aka kashe a hare-hare tun shekarar 2023. Ƙungiyar ta kuma yi kira da a gudanar da bincike kan kashe-kashen da ake zargin sun faru a yankin.














