ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 19, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

by Abubakar Sulaiman
50 minutes ago

Shugaban Rukunin First City Monument Bank (FCMB), Ladi Balogun, ya ce fara sayar da hannayen jarin Matatar Dangote ga jama’a ya buɗe wa ’yan Nijeriya damar zuba jari a wani babban kamfani mai matakin kasuwanci na duniya, tare da tallata yadda kasuwar hada-hadar hannayen jari ta ƙasa ke ƙara faɗaɗa. Ya bayyana hakan ne a yayin da aka fara karɓar kuɗin masu son sayen hannayen jarin a kasuwar sayar da hannun jari ta Nijeriya da ke Legas.

Matatar Dangote ta fitar da hannun jari biliyan 4.1 a farashin Naira 525 kan kowane hannu, wanda zai iya samar da kusan Naira tiriliyan 2.15 idan an sayar da su baki ɗaya. An buɗe tayin ne ranar 14 ga Satumba 2026, kuma za a rufe shi ranar 13 ga Oktoba 2026. Mafi ƙarancin hannun jarin da mutum zai iya saya shi ne guda 10, wanda ke a farashin Naira 5,250.

Balogun ya ce tayin ya samar da damar da ɗaiɗaikun ƴan Nijeriya za su iya shiga zuba jari a manyan kamfanoni, yayin da masu zuba jari daban-daban, ciki har da ƙananan masu zuba jari, da attajirai, da cibiyoyin zuba jari da masu zuba jari daga ƙasashen waje ke ƙara shiga kasuwar. Ya ce ƙarin hanyoyin sayen hannayen jari ta bankuna, da dillalan hannayen jari da kafafen fintech na taimaka wa jama’a su shiga kasuwar cikin sauƙi.

ADVERTISEMENT

FCMB Group na da hannu a cikin tayin ta kamfanoninsa guda uku: FCMB Capital Markets a matsayin ɗaya daga cikin masu shirya bayar da hannayen jarin, da CSL Stockbrokers a matsayin dillalin hannayen jarin, sannan First City Monument Bank a matsayin bankin karɓar kuɗi da rarraba hannayen jarin.

Matatar Dangote tana da ikon tace ganga 700,000 na ɗanyen mai a kowace rana, kuma tana da shirin ƙara ƙarfin tace man zuwa kusan ganga miliyan 1.4 a kowace rana. A cewar shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, an tsara tayin ne domin faɗaɗa mallakar matatar, ta yadda ƴan Nijeriya daga sassa da matakan samun kuɗi daban-daban za su samu damar mallakar wani kaso na kamfanin.

LABARAI MASU NASABA

Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa
  • Abubakar Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano
  • Abubakar Sulaiman
    ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi
  • Abubakar Sulaiman
    Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

MASU ALAKA

Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa
Labarai

Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa

September 19, 2026
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano

September 19, 2026
Atiku Ga Tinubu: Fada Wa ‘Yan Nijeriya Yadda Ka Samu Digiri Ba Tare Da Firamare Da Sakandare Ba
Manyan Labarai

Atiku Ya Nemi Tinubu Ya Rage Farashin Man Fetur Don Sauƙaƙa Wa ’Yan Nijeriya Wahalar Da Suke Sha

September 18, 2026

LABARAI MASU NASABA

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

September 19, 2026
Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa

Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa

September 19, 2026
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano

September 19, 2026
Yadda Amurka Ta Mayar Wa Sin Da Kayan Tarihi Ya Nuna Kyakkyawan Fata Na Gina Dangantaka Mai Inganci A Tsakaninsu

Yadda Amurka Ta Mayar Wa Sin Da Kayan Tarihi Ya Nuna Kyakkyawan Fata Na Gina Dangantaka Mai Inganci A Tsakaninsu

September 18, 2026
Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai

Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai

September 18, 2026
Atiku Ga Tinubu: Fada Wa ‘Yan Nijeriya Yadda Ka Samu Digiri Ba Tare Da Firamare Da Sakandare Ba

Atiku Ya Nemi Tinubu Ya Rage Farashin Man Fetur Don Sauƙaƙa Wa ’Yan Nijeriya Wahalar Da Suke Sha

September 18, 2026
Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

September 18, 2026
Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

September 18, 2026
‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

Neja: An Fesa Wani Abu A Ɗakin Da Aka Tsare Mu – Matashin Da Ya Tsira

September 18, 2026
Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan

Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan

September 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.