Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki matakin gaggawa wajen rage farashin man fetur, yana mai cewa hauhawar farashin makamashi na ƙara tsadar sufuri, da abinci da sauran kayayyaki a Nijeriya.
Atiku ya yi wannan kiran ne ranar Juma’a a Abuja yayin da yake magana kan farashin mai, da tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa da kuma matsin tattalin arziƙin da ƴan ƙasa ke fuskanta.
Atiku ya ce cire tallafin man fetur tun ranar 29 ga Mayu, 2023 ya jefa iyalai, ma’aikata, da manoma da ƴan kasuwa cikin ƙarin nauyin rayuwa, musamman saboda tashin farashin sufuri da kayan abinci. Ya ce idan farashin makamashi ya tashi, farashin sufuri da samar da kayayyaki ma na tashi, lamarin da a cewarsa ke ƙara rage ƙarfin darajar Naira.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma soki dogaro da tallafin gaggawa wajen rage raɗaɗin tsadar rayuwa, yana mai cewa irin wannan tallafi ba zai maye gurbin manufofin da za su magance tushen matsalar tsadar kayayyaki ba. Ya kuma tunatar da Tinubu cewa a baya ya yi watsi da kiransa na rage farashin mai, inda ya ce shugaban ƙasar ya bayyana shawarar a matsayin wadda ke nuna rashin fahimtar yadda gwamnati da tattalin arziƙi ke aiki.
Atiku ya kuma yi gargaɗi kan shirin gwamnatin tarayya na janye tallafin wutar lantarki daga shekarar 2027, yana mai cewa bai kamata a sake maimaita abin da ya biyo bayan cire tallafin man fetur ba. Ya ce gidaje, da ƙananan ’yan kasuwa da masana’antu sun riga sun fuskanci tsadar wutar lantarki da dizal, don haka cire tallafin ba tare da wasu matakan rage nauyin ba na iya ƙara matsin tattalin arziƙi.
Atiku ya ce a shirye yake ya bai wa gwamnatin Tinubu tsarin manufofin da zai taimaka wajen rage farashin man fetur, ko da gwamnati za ta aiwatar da shi da wani suna. Ya kuma bayyana wani shirin da ya ce zai aiwatar idan aka zaɓe shi a 2027, wanda zai ƙunshi tallafin samar da man fetur da aka tace a cikin Nijeriya, tare da sa ido da tantancewa.
Ya ce abin da ya fi muhimmanci a gare shi shi ne ƴan Nijeriya su samu sauƙin rayuwa, yana mai cewa “ku bar ’yan Nijeriya su shaƙi iska.”














