ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 19, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa

by Abubakar Sulaiman
2 hours ago

Ƙungiyar Nigeria Forward Project ta yi kira ga ƴan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a Arewacin Nijeriya da su mutunta tsarin karɓa karɓa, tare da barin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adin shekaru takwas kafin Arewa ta nemi komawa kan kujerar shugaban ƙasa.

An bayyana wannan matsaya ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin bikin ƙaddamar da ƙungiyar Nigeria Forward, wadda ta ce an kafa ta ne domin inganta haɗin kan ƙasa, da ƙarfafa shigar ’yan ƙasa cikin harkokin mulki da kuma tallafa wa ci gaba da manufofin gwamnati gabanin zaɓen 2027 da bayan sa.

Ministan Ƙirƙire-Ƙirƙire, da Kimiyya da Fasaha, kuma jagoran yunƙurin, Dr Kingsley Tochukwu Udeh, ya ce manufofin gwamnati na yanzu na neman sauya tattalin arziƙin ƙasar daga gyare-gyare zuwa samar da ababen more rayuwa, sannan zuwa samar da ayyukan yi. Ya ce ƙungiyar za ta taimaka wajen isar da bayanai kan ayyukan gwamnati, da zuba jari da samar da damarmaki ga ƴan ƙasa.

ADVERTISEMENT

A nasa ɓangaren, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, kuma ɗaya daga cikin jagororin kafa ƙungiyar, Ibrahim Waiya, ya ce bai kamata Arewa ta nemi komawa fadar shugaban ƙasa bayan wa’adi guda na gwamnatin Tinubu ba. Ya ce kammala shekaru takwas zai ba gwamnati damar ci gaba da manufofinta da kuma ƙarfafa abin da ta fara.

Waiya ya kuma ambaci cin gashin kan ƙananan hukumomi, da ƙarin kuɗaɗen da ke zuwa ga ƙananan hukumomi da jihohi, da shirin kafa ƴansandan jihohi a matsayin wasu daga cikin sauye-sauyen da ya ce za su iya inganta mulki da tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano

Waiya ya ƙara da cewa ya kamata a daina kallon matsalolin talauci da ci gaban Arewacin Nijeriya a matsayin nauyin shugaban ƙasa kaɗai, yana mai cewa dimokuraɗiyya na buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, da ta ƴan ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB
  • Abubakar Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano
  • Abubakar Sulaiman
    ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi
  • Abubakar Sulaiman
    Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

MASU ALAKA

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB
Labarai

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

September 19, 2026
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano

September 19, 2026
Atiku Ga Tinubu: Fada Wa ‘Yan Nijeriya Yadda Ka Samu Digiri Ba Tare Da Firamare Da Sakandare Ba
Manyan Labarai

Atiku Ya Nemi Tinubu Ya Rage Farashin Man Fetur Don Sauƙaƙa Wa ’Yan Nijeriya Wahalar Da Suke Sha

September 18, 2026
Next Post
Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido - FCMB

LABARAI MASU NASABA

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Buɗe Wa Ƴan Nijeriya Ido – FCMB

September 19, 2026
Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa

Ku Bar Tinubu Ya Kammala Shekaru 8, Nigeria Forward Ta Nemi Ƴan Siyasar Arewa

September 19, 2026
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Dagaci A Kano

September 19, 2026
Yadda Amurka Ta Mayar Wa Sin Da Kayan Tarihi Ya Nuna Kyakkyawan Fata Na Gina Dangantaka Mai Inganci A Tsakaninsu

Yadda Amurka Ta Mayar Wa Sin Da Kayan Tarihi Ya Nuna Kyakkyawan Fata Na Gina Dangantaka Mai Inganci A Tsakaninsu

September 18, 2026
Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai

Sin Ta Bukaci Japan Ta Fuskanci Tarihinta Na Mamayar Zalunci Tare Da Waiwaye Mai Zurfi A Kai

September 18, 2026
Atiku Ga Tinubu: Fada Wa ‘Yan Nijeriya Yadda Ka Samu Digiri Ba Tare Da Firamare Da Sakandare Ba

Atiku Ya Nemi Tinubu Ya Rage Farashin Man Fetur Don Sauƙaƙa Wa ’Yan Nijeriya Wahalar Da Suke Sha

September 18, 2026
Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

Kasar Sin Ta Samu Jarin Waje Kimanin Yuan Biliyan 479.95 A Watanni 8 Na FarkonBana

September 18, 2026
Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

Sana’ar Aike Da Sakwanni a Sin Ta Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Kwanciyar Hankali

September 18, 2026
‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

Neja: An Fesa Wani Abu A Ɗakin Da Aka Tsare Mu – Matashin Da Ya Tsira

September 18, 2026
Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan

Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Tuntubar Juna Game Da Shirye-shiryen Ganawar Shugabannin Kasashen Biyu Cikin Shekarar Nan

September 18, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.