Yau Laraba, aka fitar da jigo da tambarin shirye-shiryen murnar bikin sabuwar shekarar Sinawa na 2026, wato Bikin Bazara na shekarar doki na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG. Za a gudanar da bikin bisa jigon “Ba za a iya tsayar da gudun dawaki ba” cikin yanayi na farin ciki da jin dadi, ta yadda Sinawa a duk fadin duniya za su iya haduwa a wannan gaggarumin biki mai ban sha’awa dake cike da kuzari da kuma farin ciki.
A wannan sabuwar shekarar da za a soma gudanar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15, shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG za su taya jama’ar kasar Sin dake duk fadin duniya maraba da sabuwar shekarar doki bisa kalandar gargajiyar kasar mai cike da kuzari da albarka da farin ciki. (Bilkisu Xin)














