An bude taron hadin gwiwar kafafen yada labarai na Sin da Afirka karo na 7 a yau 20 ga watan Agusta a birnin Beijing, inda manyan baki na matakin minista guda 33 daga kasashen Afirka suka halarta, inda ya zama mafi girma a tarihi. An kuma fitar da “Sanarwar hadin gwiwa ta taron”.
Mahalarta taron sun bayyana cewa, kafafen yada labarai na Sin da Afirka za su ci gaba da zama gadar musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka, kana za su karfafa hadin gwiwa a mabambantan bangarori tsakanin Sin da Afirka bisa karfinsu na yada labarai, kazalika za su fadada hadin gwiwa a sabbin nau’ikan ayyuka kamar gajerun fina-finan wasan kwaikwayo da sauransu, har da karfafa aikin ba da labarai tare da fassara da watsa shirye-shirye tsakaninsu, ta yadda za su inganta zumuncin jama’ar Sin da Afirka ta ingantattun abubuwan da za su samar.
Ban da wannan kuma, za su karfafa hadin gwiwa a fannin amfani da sarrafa AI, da kuma ciyar da ci gaban kafafen yada labarai na Sin da Afirka gaba ta hanyar kirkire-kirkiren fasahar zamani, da kuma karfafa musayar manyan jami’ai da jama’a da matasa, da zurfafa koyi da juna tsakaninsu ta hanyar musayar ma’aikata. (Amina Xu)














