Da safiyar yau ne aka gudanar da taron ministocin noma kan samar da isasshen abinci na kungiyar APEC karo na 11 a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang, a matsayin daya daga cikin jerin ayyukan “shekarar Sin ta APEC”, kuma taron ya kasance daya daga manyan tarukan ministoci na yankin Asiya da tekun Pasifik a fannin noma, kana mafi girma da kuma fadi a bana.
Kazalika, taron ya mayar da hankali kan batutuwa masu muhimmanci, kamar “hada kai don inganta ci gaban aikin noma da raya karkara na yankin Asiya da tekun Pasifik tare”, da “karfafa aikin samar da isashen abinci ta amfani da kirkire-kirkire da fasahar AI a fannin noma”.
Kana zai samar da damar karfafa mu’ammalar kwarewa, da zurfafa musayar manufofi, da kuma ciyar da hadin gwiwa a mabambantan bangarori na noma gaba, a fannoni kamar inganta karfin aikin noma, da saukake cinikayyar kayayyakin noma na yanki, da farfado da karkara da amfani da AI a fannin noma, ta yadda za a samar da isashen abinci cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)














