ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Zai Ƙaddamar Da Jirgin Ƙasan Kaduna–Kano Ranar 3 Ga Disamba

by Abubakar Sulaiman
4 hours ago

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai ƙaddamar da sashin layin dogo mai tsawon kilomita 190 daga Jaji zuwa Kano, wanda aka kammala a matsayin wani ɓangare na aikin layin dogon Kaduna–Kano, a ranar 3 ga Disamba, 2026. Dele Alake, mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba.

Alake ya ce aikin layin dogon mai tsawon kilomita 203 ya kai kusan kashi 90 cikin 100 na kammalawa. Layin dogon Kaduna–Kano ƙari ne ga layin dogo mai amfani da ma’auni na zamani (standard gauge) da ya haɗa Abuja da Kaduna. Idan aka kammala shi gaba ɗaya, zai haɗa Abuja, Kaduna, Zariya da Kano, tare da samar da wata hanyar sufuri ta daban a kan muhimmin hanyar kasuwanci da ke Arewacin Nijeriya.

Ya kuma bayyana cewa aikin layin dogon Kano–Katsina–Maradi mai tsawon kilomita 400 ya kai kashi 70 cikin 100 na kammalawa. A cewarsa, wata tawagar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Funso Adebiyi, Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, ta gudanar da rangadin duba ayyukan biyu bisa umarnin Shugaba Tinubu.

ADVERTISEMENT

Alake ya ce tawagar ta nuna gamsuwa da ingancin aikin, musamman yadda aka shimfiɗa gwadaben, da magudanan ruwa, da kariyar tudu, da shimfiɗar ƙananan duwatsu da kuma matakan ƙarfafa ƙasa. Tawagar ta kuma yi gwajin tafiya a jirgin ƙasan daga Jaji a Jihar Kaduna zuwa Kano domin tantance ingancin layin da aka kammala da kuma jin daɗin fasinjoji yayin tafiya.

Ya ƙara da cewa Tinubu ya bayar da umarnin warware matsalolin rikicin mallakar filaye da biyan diyya da suka rage a cikin birnin Kaduna cikin gaggawa, domin a samu damar kammala hanyar layin dogon da za ta haɗa Abuja da Kano.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Bindiga Suka Ƙone Mutane 12 Ƴan Gida Ɗaya A Zamfara

Tsoron Faɗuwa Zaɓe Ne Ya Sa Tinubu Jinkirta Karɓar Haraji – Kwankwaso

Haka kuma, za a ƙaddamar da sashin aikin layin dogon Kano–Maradi mai tsawon kilomita 250, daga Dawanu zuwa Kano, Kazaure, zuwa Daura da Katsina, a ranar 3 ga Disamba.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Yadda Ƴan Bindiga Suka Ƙone Mutane 12 Ƴan Gida Ɗaya A Zamfara
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Za Ta Tattauna Kan Makomar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar ADC
  • Abubakar Sulaiman
    Tsoron Faɗuwa Zaɓe Ne Ya Sa Tinubu Jinkirta Karɓar Haraji – Kwankwaso
  • Abubakar Sulaiman
    Tsadar Hayar Shaguna Ya Sa Ƴan Kasuwar Abuja Sun Koma Sayar Da Kaya Ta Intanet

MASU ALAKA

Yadda Ƴan Bindiga Suka Ƙone Mutane 12 Ƴan Gida Ɗaya A Zamfara
Labarai

Yadda Ƴan Bindiga Suka Ƙone Mutane 12 Ƴan Gida Ɗaya A Zamfara

November 8, 2026

Next Post
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Salon Shugabancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Ghana

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Salon Shugabancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Ghana

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Bindiga Suka Ƙone Mutane 12 Ƴan Gida Ɗaya A Zamfara

Yadda Ƴan Bindiga Suka Ƙone Mutane 12 Ƴan Gida Ɗaya A Zamfara

November 8, 2026
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Salon Shugabancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Ghana

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Salon Shugabancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Ghana

November 8, 2026
Tinubu Zai Ƙaddamar Da Jirgin Ƙasan Kaduna–Kano Ranar 3 Ga Disamba

Tinubu Zai Ƙaddamar Da Jirgin Ƙasan Kaduna–Kano Ranar 3 Ga Disamba

November 8, 2026
CIIE Na Bai Wa Duniya Damar Cin Gajiyar Manufar Sin Ta Bude Kofa Ga Waje

CIIE Na Bai Wa Duniya Damar Cin Gajiyar Manufar Sin Ta Bude Kofa Ga Waje

November 8, 2026
Tsoron Faɗuwa Zaɓe Ne Ya Sa Tinubu Jinkirta Karɓar Haraji – Kwankwaso

INEC Za Ta Tattauna Kan Makomar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar ADC

November 8, 2026
Sin Ta Gudanar Da Bikin Cika Shekaru 55 Da Maido Mata Halastacciyar Kujerarta Ta MDD

Sin Ta Gudanar Da Bikin Cika Shekaru 55 Da Maido Mata Halastacciyar Kujerarta Ta MDD

November 8, 2026
Tsoron Faɗuwa Zaɓe Ne Ya Sa Tinubu Jinkirta Karɓar Haraji – Kwankwaso

Tsoron Faɗuwa Zaɓe Ne Ya Sa Tinubu Jinkirta Karɓar Haraji – Kwankwaso

November 8, 2026
An Kaddamar Da Taron Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 7 A Birnin Beijing

An Kaddamar Da Taron Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 7 A Birnin Beijing

November 8, 2026
Tsadar Hayar Shaguna Ya Sa Ƴan Kasuwar Abuja Sun Koma Sayar Da Kaya Ta Intanet

Tsadar Hayar Shaguna Ya Sa Ƴan Kasuwar Abuja Sun Koma Sayar Da Kaya Ta Intanet

November 8, 2026
Ƴansanda Sun Kwato Shanu 39 Da Aka Sace Bayan Musayar Wuta Da Barayin Shanu

Ƴansanda Sun Kwato Shanu 39 Da Aka Sace Bayan Musayar Wuta Da Barayin Shanu

November 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.