Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jinkirta fara karɓar haraji bisa sabbin dokokin haraji saboda tsoron fuskantar fushin masu zaɓe a babban zaɓen 2027. Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen NDC a Jihar Jigawa, wanda aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar.
Tsohon gwamnan Kano ya ce duk da cewa Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da ƙudurin dokokin harajin, gwamnatin tarayya na jan ƙafa wajen fara aiwatar da su saboda fargabar cewa hakan zai rage mata farin jini gabanin zaɓen 2027. Ya yi zargin cewa idan jam’iyyar APC ta sake samun nasarar lashe zaɓe, ƴan Nijeriya za su fuskanci ƙarin haraji mai yawa.
Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa sabbin dokokin za su iya jefa jama’a cikin ƙarin matsin tattalin arziƙi, yana mai cewa gwamnati za ta iya tsaurara hanyoyin karɓar haraji har zuwa binciken gidajen mutane. Ya kuma soki yadda aka amince da dokokin a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, yana zargin wasu ƴan majalisa da amincewa da ƙudurin ba tare da la’akari da tasirinsa ga talakawa ba.
Ya kuma yi zargin cewa Shugaban Majalisar Dattawa ya ƙaurace wa zaman da aka tattauna tare da amincewa da ƙudurin harajin da gangan domin kauce wa alaƙa da matakin.
Kwankwaso ya ce idan aka zaɓi NDC, jam’iyyar za ta soke harajin da ta kira marasa amfani, ta inganta ilimi tare da ɗaukar nauyin karatun yara. Ya kuma buƙaci ƴan Nijeriya kada su sake bai wa APC dama ta ci gaba da mulki, yana mai cewa zaɓen 2027 zai zama dama ga jama’a su yanke shawarar makomar ƙasar.













