Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta sun daƙile wani harin satar shanu tare da ƙwato shanu 39 a ƙauyen Illa, da ke Ƙaramar Hukumar Igabi ta jihar. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, lokacin da wasu mahara ɗauke da makamai suka kai hari ƙauyen tare da sace shanun wasu makiyaya Fulani uku.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Kaduna cewa jami’in ƴansanda na sashin Rigachikun ya samu kiran gaggawa daga wani mazaunin ƙauyen mai suna Alhaji Yahaya Abubakar da misalin ƙarfe 5 na Asuba. Ya ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 4 na asuba, inda suka sace shanun tare da harbin wani matashi mai shekara 25 mai suna Abubakar a ƙafafunsa biyu.
Hassan ya ce bayan samun rahoton, jami’an ƴansanda ƙarƙashin jagorancin shugaban ofishin Amana, tare da jami’an tsaron sa-kai na yankin da mazauna ƙauyen, sun bi sawun maharan har cikin daji. Ya bayyana cewa an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da waɗanda ake zargin masu satar shanun ne, lamarin da ya tilasta musu ɓarayin shanun 39 ɗin da guduwa cikin daji.
Ya ƙara da cewa maharan sun tsere ne da raunukan harbin bindiga. Matashin da aka harba kuwa an garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Shika, inda yake samun kulawa kuma yanayin lafiyarsa na inganta. Rundunar ta tabbatar da cewa an mayar da shanun da aka ƙwato ga masu su.
Kwamishinan Ƴansandan jihar, CP Muhammad Rabiu, ya yaba wa jami’an tsaro da mazauna yankin bisa haɗin gwiwar da suka bayar wajen daƙile harin. Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa ayyukanta domin yaƙi da satar shanu da sauran laifuffuka a jihar.














