ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Za Ta Tattauna Kan Makomar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar ADC

by Abubakar Sulaiman
8 hours ago
INEC

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta gudanar da taro a mako mai zuwa domin nazarin tasirin hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, ciki har da batun zaɓen tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe na INEC, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan ranar Lahadi. Ya ce hukumar ba za ta yanke matsaya kan rikicin shugabancin ADC ba har sai ta samu kwafin hukuncin kotun da aka tabbatar da sahihancinsa (Certified True Copy), domin ba za ta dogara da rahotannin kafafen yaɗa labarai wajen fassara hukuncin ba.

Hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke a Abuja ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026, ya soke shugabancin kwamitin riƙon ƙwarya na David Mark tare da rushe matakan da kwamitin ya ɗauka. Hakan ya haɗa da zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, da kuma naɗin Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.

ADVERTISEMENT

Shari’ar ta samo asali ne daga ƙarar da tsohon Mataimakin Shugaban ADC na Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar, inda ya ƙalubalanci yadda David Mark da sauran mambobin kwamitin riƙon ƙwarya suka karɓi shugabancin jam’iyyar. Gombe ya yi iƙirarin cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, kundin tsarin mulkin ADC ya ba shi damar karɓar ragamar shugabancin.

Haruna ya ce INEC za ta tattauna batun a taronta na mako mai zuwa, kuma za ta bi duk wani sabon umarnin kotu idan ɓangaren David Mark ya ɗaukaka ƙara tare da samun umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin. A halin yanzu, hukuncin kotun ya jefa shakku kan sahihancin tikitin Atiku da sauran ƴan takarar da aka tsayar ƙarƙashin shugabancin da aka soke.

LABARAI MASU NASABA

Dimokuraɗiyyar Nijeriya Na Cikin Tasku – Yusuf Dantalle

Ku Karɓi Kuɗin APC, Amma Ku Fatattake Su A 2027, Makinde Ya Buƙaci ’Yan Nijeriya

INEC
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Yadda Ƴan Bindiga Suka Ƙone Mutane 12 Ƴan Gida Ɗaya A Zamfara
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Zai Ƙaddamar Da Jirgin Ƙasan Kaduna–Kano Ranar 3 Ga Disamba
  • Abubakar Sulaiman
    Tsoron Faɗuwa Zaɓe Ne Ya Sa Tinubu Jinkirta Karɓar Haraji – Kwankwaso
  • Abubakar Sulaiman
    Tsadar Hayar Shaguna Ya Sa Ƴan Kasuwar Abuja Sun Koma Sayar Da Kaya Ta Intanet

MASU ALAKA

Dimokuraɗiyyar Nijeriya Na Cikin Tasku – Yusuf Dantalle
Siyasa

Dimokuraɗiyyar Nijeriya Na Cikin Tasku – Yusuf Dantalle

November 7, 2026
Ku Karɓi Kuɗin APC, Amma Ku Fatattake Su A 2027, Makinde Ya Buƙaci ’Yan Nijeriya
Siyasa

Ku Karɓi Kuɗin APC, Amma Ku Fatattake Su A 2027, Makinde Ya Buƙaci ’Yan Nijeriya

November 7, 2026
Tinubu Ya Yi Wa Peter Obi Shaguɓe Kan Matsalar Zaizayar Ƙasa A Anambra
Siyasa

Tinubu Ya Yi Wa Peter Obi Shaguɓe Kan Matsalar Zaizayar Ƙasa A Anambra

November 7, 2026
Next Post
CIIE Na Bai Wa Duniya Damar Cin Gajiyar Manufar Sin Ta Bude Kofa Ga Waje

CIIE Na Bai Wa Duniya Damar Cin Gajiyar Manufar Sin Ta Bude Kofa Ga Waje

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Bindiga Suka Ƙone Mutane 12 Ƴan Gida Ɗaya A Zamfara

Yadda Ƴan Bindiga Suka Ƙone Mutane 12 Ƴan Gida Ɗaya A Zamfara

November 8, 2026
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Salon Shugabancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Ghana

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Salon Shugabancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Ghana

November 8, 2026
Tinubu Zai Ƙaddamar Da Jirgin Ƙasan Kaduna–Kano Ranar 3 Ga Disamba

Tinubu Zai Ƙaddamar Da Jirgin Ƙasan Kaduna–Kano Ranar 3 Ga Disamba

November 8, 2026
CIIE Na Bai Wa Duniya Damar Cin Gajiyar Manufar Sin Ta Bude Kofa Ga Waje

CIIE Na Bai Wa Duniya Damar Cin Gajiyar Manufar Sin Ta Bude Kofa Ga Waje

November 8, 2026
Tsoron Faɗuwa Zaɓe Ne Ya Sa Tinubu Jinkirta Karɓar Haraji – Kwankwaso

INEC Za Ta Tattauna Kan Makomar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar ADC

November 8, 2026
Sin Ta Gudanar Da Bikin Cika Shekaru 55 Da Maido Mata Halastacciyar Kujerarta Ta MDD

Sin Ta Gudanar Da Bikin Cika Shekaru 55 Da Maido Mata Halastacciyar Kujerarta Ta MDD

November 8, 2026
Tsoron Faɗuwa Zaɓe Ne Ya Sa Tinubu Jinkirta Karɓar Haraji – Kwankwaso

Tsoron Faɗuwa Zaɓe Ne Ya Sa Tinubu Jinkirta Karɓar Haraji – Kwankwaso

November 8, 2026
An Kaddamar Da Taron Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 7 A Birnin Beijing

An Kaddamar Da Taron Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 7 A Birnin Beijing

November 8, 2026
Tsadar Hayar Shaguna Ya Sa Ƴan Kasuwar Abuja Sun Koma Sayar Da Kaya Ta Intanet

Tsadar Hayar Shaguna Ya Sa Ƴan Kasuwar Abuja Sun Koma Sayar Da Kaya Ta Intanet

November 8, 2026
Ƴansanda Sun Kwato Shanu 39 Da Aka Sace Bayan Musayar Wuta Da Barayin Shanu

Ƴansanda Sun Kwato Shanu 39 Da Aka Sace Bayan Musayar Wuta Da Barayin Shanu

November 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.