Wasu ƴan bindiga sun kashe mutane 12 iyalin gida guda bayan sun cinna wa ɗakin da suka fake a ciki wuta a ƙauyen Gidan Taba, da ke Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara. Harin ya faru ne a daren Asabar, a unguwar Dosara Birnin Kaya, inda maharan suka kuma sace wasu mazauna yankin.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Daily Trust cewa iyalan Mallam Muhammadu Sani sun kulle kansu a cikin ɗaki guda ne domin guje wa sace su. Sai dai bayan ƴan bindigar sun gano inda suke, sun umarce su da su buɗe ƙofar, amma suka ƙi. Daga nan ne maharan suka cinna wa ɗakin wuta.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Maradun, Sanusi Ahmed Dosara, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici da rashin imani. Ya ce waɗanda suka mutu sun haɗa da uba, da matansa da ƙananan ƴaƴansa. A cewarsa, zafin wutar ne ya yi sanadin mutuwarsu, ba wai lallai harshen wutar ne ya ƙone su kai tsaye ba.
Dosara ya kuma tabbatar da cewa maharan sun yi awon gaba da wasu mazauna ƙauyen, amma ƴan sa-kai sun yi arangama da su tare da samun nasarar kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sace. Ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da ke hannun ƴan bindigar ba saboda halin tashin hankalin da ake ciki a yankin.
An gudanar da jana’izar mutum 12 ɗin a safiyar Lahadi bisa tsarin addinin Musulunci, inda shugaban ƙaramar hukumar ya jagoranci sallar jana’izarsu. Ya kuma ce maharan sun riƙa harbe-harbe ta wurare daban-daban domin rikitar da jami’an tsaro, tare da bayyana cewa ya ziyarci sansanin ƴansanda mafi kusa domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da hana sake aukuwar irin wannan hari.












