An samu tashin hankali a garin Asaba, Jihar Delta, ranar Asabar, bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar NDC da ke gudanar da tattakin mutum miliyan ɗaya domin nuna goyon baya ga takarar Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Rahotanni sun ce mutane da dama sun jikkata, yayin da aka lalata motocin kamfen da ke ɗauke da hotunan Obi, mataimakinsa Kwankwaso da ɗan takarar sanatan Delta ta Arewa, Victor Ochei.
Lamarin ya faru ne bayan makamancin wannan hari da ya kawo cikas ga gangamin jam’iyyar a Effurun, cikin Jihar Delta.Rahoton ya ce waɗanda ake zargin sun kai harin sun yi amfani da sanduna, wuƙaƙe, adduna da wasu makamai. An kuma ga wasu mutane suna dukan waɗanda ake zargin maharan ne bayan an cafke su yayin rikicin.
Da yake mayar da martani, Victor Ochei, tsohon kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, ya buƙaci Gwamna Sheriff Oborevwori da ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da kama waɗanda ke da hannu a harin.
Ochei ya bayyana harin a matsayin abin Allah-wadai, inda ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da amfani da tsoratarwa maimakon fafatawa ta hanyar gabatar da manufofi da ayyukan da ta gudanar.
Ya kuma yi zargin cewa an lalata motocin kamfen sama da 30, yana mai cewa wasu masu tuka adaidaita sahu ne suka jagoranci harin ƙarƙashin kulawar wani shugaban ƙungiya da ke kula da harkokin adaidaita sahu a jihar.













