Masana’antar Kannywood tana samun gagarumin sauyi, a halin yanzu, hakan na zuwa ne yayin da ake kara samun wasu jarumai mata.
Irin waxannan sabbin fuskokin jaruman mata, sun nuna kwazo da zai sa su ci gaba a harkar.
Wannan sharhin zai yi duba ne kan jeren jarumai mata da masu bibiyar masana’antar ke ganin za su ja zarensu a shekarar 2027.
Aisha Soba:
Ta farkonsu daga cikin wannan jeren ita ce, Aisha Soba, wacce kuma ta na xaya daga cikin sabbin fuskokin da suka yi fice cikin sauri a Kannywood.
Soba, har ta kai ga shiga cikin jerin rukunin jarumai mata da ke a kan gaba wajen fitowa a cikin fina-finai”.
Kazalika jarumar ta shahara wajen iya fitar da tsarin da aka ba ta cikin natsuwa.
Tauraronta ya fara haskawa ne a shekarar ta 2025, inda ta fito a wasu fitattun wakoki, kamar irin su ‘Makauniya’ da Auta MG ya rera wakar kamfanin Arewa Medium ya xauki nauyin fim xin, inda ta fito, a matsayin makauniya a bidiyon wakar.
Fatima Ibrahim:
Matashiyar jarumar, tauraruwa ce da ke kara samun karvuwa a wurin masu kallo musamamn masoyanta.
Jarumar na samun karvuwar ne saboda karsashi da kuma kwarewa a fina-finai na zamani, inda hakan ya sanya, ta shiga cikin jeren waxanann jarumai mata, da za su ja Zarensu a baxi.
Asmau Jika:
Ita kuwa wannan jarumar, ta kasance jigo ce, a tsakanin sabbin jarumai mata da ke tasowa.
Jarumar, ta mai kazar-kazar da kuzar, ta kuma kasance mai jini a jiki, musamman a cikin fina-finan da ta fito.
Asmau na da tasiri a fina-finan da ake saki a dandalin YouTube, wanda hakan, ya sanya, ita ma bi sahun wannan jeren.
Aisha Muhammed Jogana:

Tun bayan fitowarta a shirin Jahilan kauye, jarumar ta kuma fito a cikin wasu fina-finai masu dogon zango kamar irin su in da Ranka da Rayuwar Duniya, hakan ya sanya ta shiga cikin jeren jaruman mata, da masu kallo za su sanya ido a kansu a 2027.
Wasu daga cikin masu fashin baki a masana’antar ta Kannywood na hasashen Aisha za ta taka muhimmiyar rawa a masana’antar, a 2027.
Ummassalama Sadik:
Wannan jarumar da ake yi wa lakabi da Salma Gezawa, ta shafe lokaci tana aikin bayan fage, sai dai, Gezawa, ta fito fili a matsayin babbar jaruma a fim xin Baban Ladi.
Wannan fitowar ta Gezawa, a cikin wannan fim xin, ya zamo silar buxe mata kofar shahara.
Gezawa, ‘yar asalin Jihar Kano ta shiga harkar fin ne, bayan kammala makarantar Sakandare.
Shahararren jaruma Yahanasu Sani ce, ta fara kawo ta masana’antar Kannywood, Gezawa fitowarta a cikin fina-finai da suka kara mata masoya masu kallo da kuma a tsakanin wasu masu gabatarwa a masana’antar.
Shigar Gezawa Kannywood da kafar dama, musamman yadda wasu masu Kallon fina-finan da ta fito, hakan ya sanya, jarumar, ta shiga cikin jeren jarumai mata, da za su ja Zarensu, a 2027.
Amina Muhammad Rabi’u:
Jaruma Amina wadda ake yi wa lakabi da Ikiram Labarina sabuwar jaruma ce da ta taka rawa a fim xin na Labarina.
Fitowar da ta yi a cikin fim xin ne, ya sanya ake yi mata lakabi da Ikram, domin da wannan sunan ne ake kiranta a cikin fim xin.
Amina ‘yar asalin karamar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, fim xinta na farko shi ne, Lubna da aka yi kusan shekara huxu da suka gabata.
Sai dai a cikin fim xin Labarina zangon da aka yi a wannan shekarar ne ya haskaka ta a idon duniyar fina-finai.
Kazalika ta kuma fito a cikin fina-finai kamar irinsu, Jamilun Jiddan da Izzar So da sauran fina-finai da dama.
Hassana Ibrahim Rano:
Wannan jarumar ‘yar asalin Jihar Kano ce, kuma ana yi mata ake lakabi da Safiyya Zavi biyu.
Wannan fin xin, shi ne, na farko, wanda tashar Arewa24 ta shirya kuma ta xauki nauyi.
Biyo bayan irin rawar da Hassana Ibrahim Rano taka a cikin fin xin, ya sanya an yaba mata, sannan ta bayyana cewa a shirye take ta ci gaba a fitowa a wasu fina-finan, wanda hakan ya sanya, ta shiga cikin wannan jaren matan jarumai.
Amina Shehu Lulu:
Wannan jarumar, tauraronta ya kara fitowa fili a wannan shekarar 2025, wacce ta kuma taka rawar gani sosai a fim xin “DA NA SANI” na Taskar Kannywood.
Forodusa Abdul Amart ne, ya shirya, inda ta fito a matsayin matar Aminu Momoh mai son wasa da shagwava.
Sai dai ba shi ne fim xinta na farko ba kasancewarta ta fito a wasu fina-finan daban.
Fim xin kamfanin Abnur da jarumar ta fito a cikinsa, ya kara fito da basira da kuma kwarewar a fi













